25/07/2025
RAYUWA KENAN A Shekarun Baya Na Yi Tashen Da Babu Irin Abinda Ban Mallaka Ba A Masana'antar Fim, Amma Yanzu Har Gudun Saka Ni A Fim Ake Yi Saboda Ana Kallo Na Da Kuskuren Da Na Yi A Baya, Cewar Ummi Nuhu
Ummi Nuhu ta kara da cewa duk da cewa tana kaunar harkar fim har yanzu, amma koda ta je neman a saka ta a fim, sai a ki saka ta, saboda ana waiwayar kuskuren da ta yi a baya.
Cikin kuka Ummi, ta ce a yanzu ba ta da wata sana'a da ta iya illa harkar fim gashi kuma an daina yi da ita, kuma tana fama da rashin lafiya wanda ya k**ata a ce ana saka ta a fim domin ta kula da kanta.
Tsohuwar jarumar dai ta bayyana hakan ne a hirar ta da Hadiza Gabon a shorinta na 'Gabon Talk Shaw', k**ar yadda Rariya ta nakalto.
Wani karin abin tausayi a lamarin Ummi Nuhu shine, ta ce har yanzu ba ta taba yin aure ba, duk da cewa shekarunta sun ja.