Zinariya news

Zinariya news Zinariya
(2)

JIN RA'AYI: Shin Kana Ɗaya Daga Cikin Ƴan Arewa Da Zasu Iya Zaɓar Shugaba Tinubu Ya Zarce Sabo Da Kwankwaso A Zaɓen 2027...
23/07/2025

JIN RA'AYI: Shin Kana Ɗaya Daga Cikin Ƴan Arewa Da Zasu Iya Zaɓar Shugaba Tinubu Ya Zarce Sabo Da Kwankwaso A Zaɓen 2027 ?

Ku Bayyana Mana Ra'ayinku A Comment Section.

ZAƁIGWANINKA: Tsakanin Malam Nasiru El-rufa'i Da Sanata Rabi’u Musa Wa Yafi Kishin Arewa Da Talakawa?
23/07/2025

ZAƁIGWANINKA: Tsakanin Malam Nasiru El-rufa'i Da Sanata Rabi’u Musa Wa Yafi Kishin Arewa Da Talakawa?

YANZU-YANZU: Yadda Shirye-shiryen Komawar Kwankwaso APC Ya Kan K**a A Faɗin Jihar Kano Yanzu HakaMenene ra'ayinku?
23/07/2025

YANZU-YANZU: Yadda Shirye-shiryen Komawar Kwankwaso APC Ya Kan K**a A Faɗin Jihar Kano Yanzu Haka

Menene ra'ayinku?

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Omo Ovie Agege da tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Hon. ...
22/07/2025

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Omo Ovie Agege da tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Hon. Ahmad Idris Wase da sauran ƴan tawagarsu sun ziyarci gidan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ke Daura domin yi wa iyalinsa ta'aziyyar rasuwarsa.

JIYA BA YAU BA: Fuskokin Wasu Daga Cikin Ɗaliban Ɗariƙar Kwankwasiyya KenanFuskar wa kuka gane a cikin su?
22/07/2025

JIYA BA YAU BA: Fuskokin Wasu Daga Cikin Ɗaliban Ɗariƙar Kwankwasiyya Kenan

Fuskar wa kuka gane a cikin su?

Shin Kuna goyon bayan Hawa'u Halliru gwangwazo ta cigaba da fitowa a shirye shiryen gidan talabijin na RFI - Hausa ?
20/07/2025

Shin Kuna goyon bayan Hawa'u Halliru gwangwazo ta cigaba da fitowa a shirye shiryen gidan talabijin na RFI - Hausa ?

A Yau ne Alhaji Abdul Samad Rabiu ya isa Daura Domin ta'aziyya ga iyalai da makusantan Marigayi Tsohon Shugaban kasa Muh...
20/07/2025

A Yau ne Alhaji Abdul Samad Rabiu ya isa Daura Domin ta'aziyya ga iyalai da makusantan Marigayi Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

SHAWARA: Ina kira ga Tinubu ya taka wa ɗansa Seyi burki, ya daina zaƙewa kan harƙoƙin mulki, domin shekaru 8 na mulkin B...
20/07/2025

SHAWARA: Ina kira ga Tinubu ya taka wa ɗansa Seyi burki, ya daina zaƙewa kan harƙoƙin mulki, domin shekaru 8 na mulkin Buhari ban taɓa jin Yusuf ya yi magana ba sai bayan rasuwar mahaifinsa, Inji Farfesa Usman Yusuf

Me zaku ce ?

DA ƊUMI-ƊUMI: A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Kotu A Matsayin LauyaDaga Muhammad Kwairi WaziriSanata Dino Melaye,...
18/07/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: A Karon Farko Dino Melaye Ya Bayyana A Kotu A Matsayin Lauya

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Sanata Dino Melaye, wanda a kwanan nan aka tabbatar da shi a matsayin cikakken lauya, ya yi bayyanarsa ta farko a gaban alƙalin kotu a yau Alhamis.

Tsohon Sanatan na Kogi ya bayyana a gaban alkalin kotu na takwas na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, yana sanye da kayan lauya kamar yadda doka ta tanada.

Bayyanar Dino a kotu ta zo ne jim kaɗan bayan ya samu shaidar kammala karatunsa na lauya kuma ya shiga jiki-jikin masu kare hakkokin jama’a a cikin tsarin shari’a.

Wannan mataki yana nuna wani sabon babi a rayuwarsa ta siyasa da doka.

Sheik Sani Yahaya Jinhir Ne Ke Musabaha Da Su Sheik Bala Lau Da Sheik Kabiru Gombe A Wajen Zaman Makokin Buhari A Garin ...
17/07/2025

Sheik Sani Yahaya Jinhir Ne Ke Musabaha Da Su Sheik Bala Lau Da Sheik Kabiru Gombe A Wajen Zaman Makokin Buhari A Garin Daura

Allah Ya kara hada kansu.

Majalisar Dokokin Kano na shirin bincikar shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada ALGON. Sa'adatu Yusha'u.Majalisar dokokin ...
17/07/2025

Majalisar Dokokin Kano na shirin bincikar shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada ALGON. Sa'adatu Yusha'u.

Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha al’washin gudanar da bincike kan ƙorafin da wasu manoma ke yi na zargin shugabancin ƙaramar hukumar Tudun Wada karkashin jagorancin Hajiya Sa’adatu Yusha'u, kan kwace musu gonakinsu da ke Dajin Gurfa a karamar hukumar ta Tudun Wada a Kano.

‎Shugaban masu rinjaye na Majalisar Alhaji Lawan Hussain Cediyar ƴan Gurasa ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan amsa gayyatar da Majalisar ta yi wa kungiyar da ke rajin kare hakkin Ɗan-adam da tabbatar da daidaito a cikin al'umma wadda ta aike wa Majalisar korafin Manoman.

‎Da ya ke jawabi bayan amsa gayyatar da Majalisar ta yi musu, shugaban kungiyar Sa'id Bin Usman, ya ce akwai tarin korafe-korafe kan dambarwar hakkin mallaka na gonaki tsakanin shugabancin karamar hukumar Tudun Tada da kuma manoman yankin.

‎Manoma da dama ne a Dajin na Gurfa da ke yankin karamar hukumar Tudun Wada s**a shigar da korafin su kan zargin shugabar ƙaramar hukumar da ƙwace musu Gonakin su, in da kuma suke fatan majalisar dokokin jihar kano da ta duba kokensu domin samar musu da adalci.

Takaitaccen Tarihin Matar Marigayi Buhari Ta Farko, Wato Marigayiya SafinatuDaga Aliyu AhmadAn haifi Hajiya Safinatu a r...
17/07/2025

Takaitaccen Tarihin Matar Marigayi Buhari Ta Farko, Wato Marigayiya Safinatu

Daga Aliyu Ahmad

An haifi Hajiya Safinatu a ranar 11 Dec 1952 a garin Jos amma ƴar asalin karamar hukumar Mani ce a jihar Katsina, Sunan mahaifinta Alhaji Yusuf Mani mahaifiyarta kuma Hajiya Hadizatu Mani.

Shugaba Buhari ya auri marigayiya Safinatu a shekarar 1971 sannan kuma ta fara karatun firamare a Tudun Wada dake Jihar Kaduna a shekarar 1959 , ta kuma koma jihar Lagos saboda mahafinta marigayi Alhaji Yusuf Mani ya sauya sheƙar aiki zuwa jihar Lagos a matsayinsa na sakataren marigayi Musa Ƴar'adua wanda shine kwamishinan harkokin jihar Lagos a jamhuriya ta ɗaya.

Bayan kammala karatun firamare, ta halarci kwalejin malamai ta mata a jihar Katsina ,inda ba ta jima da kammala karatunta ba ta auri tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Amma shugaba Buhari ya sake ta a shekarar 1988 wanda daga bisani ya auri matarsa ta biyu wato Aisha a shekarar 1989.

Allah Ya albarkaci aurensu da ƴaƴa biyar waɗanda s**a haɗa da: Marigayiya Zulaiha, Fatima, Musa, Hadiza da Safinatu.

A shekarar 1988 marigayiya Safinatu ta kamu da ciwon siga ta kai tsawon shekaru takwas tana fama da shi, daga bisani ta rasu a shekarar 2006

Muna addu'ar da ita da mijinta, Muhammadu Buhari Allah Ya jiƙan su da gafara.

Address

Maitama

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zinariya news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zinariya news:

Share