15/05/2026
Hasashen Kimiyya Na Shekaru Da Dama Ya Gargaɗi Cewa 2026 Na Iya Zama Shekarar Da Duniya Za Ta Zo Ƙarshe
A shekarar 1960, wani masanin kimiyyar physics mai suna Heinz von Forster ya wallafa wani hasashen lissafi mai ban tsoro a mujallar Science. A cikinsa, ya yi ikirarin cewa yawan jama’ar duniya zai ruguje a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2026.
Sabanin sauran camfe-camfe ko hasashen ƙarshen duniya na buba, "Ranar Sakayya" ta von Forster ta dogara ne kan yadda yawan mutane ke ƙaruwa cikin sauri. Ya bayyana cewa idan aka ci gaba a haka, adadinmu zai wuce ƙarfin da duniyar nan za ta iya ɗauka don ciyar da mu da kuma kiyaye mu.
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a takaita wannan ƙaruwar ba, hakan zai haifar da bala’in muhalli ko kuma yaƙe-yaƙe tsakanin ƙasashe kan albarkatun ƙasa (k**ar abinci da ruwa), wanda hakan zai bar duniya a matsayin kango.
Ganin cewa ranar da ya ambata ta faɗo a ranar Juma’a 13 ga wata, wannan hasashen ya zama babban tunatarwa kan ƙalubalen da muke fuskanta wajen kula da albarkatunmu.
Yayin da masana a yau suke tattaunawa kan ko lissafin von Forster zai zama gaskiya ɗari bisa ɗari, babban saƙon da ke ciki ya kasance muhimmin jigo ga manufofin duniya. Daga batun sanya haraji ga iyalai masu yawan gaske zuwa tsauraran matakan kare muhalli, shawarwarin da aka bayar shekaru da dama da s**a wuce har yanzu suna da alaƙa da maganganun da muke yi yau game da sauyin yanayi da wadatar abinci.
Ko shekarar 2026 za ta zama lokacin rugujewar duniya ne da gaske, ko kuma dai lokaci ne na tsayawa a yi tunani, babban ƙalubalen yawan jama’a a duniyar nan yana ci gaba da zama barazana ga rayuwar ɗan Adam.
Tushen bayani: von Forster, H., Mora, P. M., & Amiot, L. W. (1960). Doomsday: Friday, 13 November, A.D. 2026. Science.
Malumfashi Reporters