
02/09/2025
SHUGABAN TINUBU YA BA DA UMARNIN ƘARFAFA TSARO A JIHAR KATSINA BAYAN ZUWAN TAWAGAR GWAMNA RADDA FADAR A*O ROCK.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa na ƙarfafa tsaro a Jihar Katsina bayan ganawar da ya yi da Gwamna Malam Dikko Umaru Radda tare da wata babbar tawaga da ta nemi agajin gwamnatin tarayya kan ƙarin tabarbarewar tsaro a jihar.
Shugaban ya umarci duka hukumomin tsaro da su sake duba dabarun yakar ‘yan ta’adda tare da ƙara tura jiragen leƙen asiri na sama (air drones), sannan ya amince da sake shirin tura dakarun ƙasa tsakanin Katsina da iyakokin jihohi domin fatattakar ‘yan ta’adda.
> “Yau na umarci hukumomin tsaro su sake karfafa dabarun da suke amfani da su. A ƙara tura jiragen leƙen asiri, sannan idan akwai buƙatar motsa dakarun tsaro tsakanin Katsina da sauran iyakokin, a yi hakan. Kuma za su ba ni rahoto nan da gobe,” in ji Shugaba Tinubu yayin taron.
Shugaban ya bayyana cewa kalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta na da matuƙar girma, inda ya ce:
> “Matsalolin tsaro da muke fuskanta a ƙasar nan sun yi yawa. Mun gaji matsalolin iyakoki marasa ƙarfi, abin da ya k**ata tun da farko a gyara. Amma wannan ƙalubale ne da dole mu fuskanta kuma muna fuskantarsa.”
Ya ƙara da cewa dakarun ƙasa za su ƙara matsa kaimi wajen kawar da miyagun ƙungiyoyi daga cikin al’umma:
> “Dakarun ƙasa suna nan, kuma za mu ci gaba da fatattakar su.”
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana aniyar gwamnatin sa na kafa ‘yan sandan jihohi a matsayin ɗaya daga cikin dabarun magance matsalolin tsaro.
> “Dole mu kare ‘ya’yanmu, mutanenmu, abincinmu, wuraren ibada da wuraren hutu. Ba za mu bari su tsoratar da mu ba,” in ji shi.
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa bisa manufar bude ƙofa da tallafin da yake bai wa Katsina a kowane lokaci:
> “Shugaba ya nuna kansa ɗan Katsina ne. Mun gode matuƙa bisa kulawar sa kan matsalolin tsaro a jiharmu,” in ji gwamnan.
A farkon taron, mai martaba Sarkin Katsina wanda Waziri na Katsina, Sanata Ibrahim Ida, ya wakilta, ya roƙi Shugaban Ƙasa da ya tabbatar da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro tare da kafa bataliyar soja da kuma rundunar ‘yan sandan MOPOL a kudancin jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe fiye da Naira biliyan 40 wajen tallafawa tsaro duk da ƙarancin kuɗaɗenta, inda ya roƙi gwamnatin tarayya ta maido mata da wani ɓangare tare da tallafa wa al’umman da s**a shiga cikin bala’in.
Tawagar da ta raka Gwamna Radda ta haɗa da mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruq Lawal Jobe; Kakakin majalisar dokoki ta jiha, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; tsohon gwamna Aminu Bello Masari; dukkan Sanatocin Katsina da wakilan majalisar tarayya.
Haka kuma akwai Ministan Ayyuka da Gidaje, Injiniya Ahmed Musa Dangiwa; Ministan Al’adu, Harshe da Tattalin Arzikin Kirkira, Barrista Hannatu Musa Musawa; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsara Manufofi, Hajiya Hadiza Bala Usman; da Jagoran AUDA-NEPAD a Najeriya, Jabiru Salisu Tsauri.
Sauran su ne: wasu mambobin majalisar zartarwa ta jihar, Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq Umar, Malam Yakubu Musa (Sautus Sunnah), tsohon mataimakin gwamnan Katsina Alhaji Tukur Jikamshi, Malam Gambo (Babban Limamin Masallacin Juma’a na Katsina), da attajirin kasuwanci Alhaji Dahiru Barau Mangal.
Wannan taro na A*o Rock ya kasance wani mataki na dabarun karshe wajen kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga da ta addabi jihar Katsina da sauran yankunan Arewa maso Yamma.