12/09/2026
ALHAMDULILLAH! 🤲
Yau, 12/09/2026, an gudanar da wani muhimmin Lecture na wayar da kan al’umma game da amfani da kafafen sada zumunta (Social Media) wajen yada labarai masu muhimmanci da amfani ga al’umma da kuma addininmu.
An tattauna yadda za a yi amfani da Social Media ta hanyar da ta dace, cikin hikima da gaskiya, domin yada abubuwan da za su taimaka wajen kawo ci gaba, wayar da kai da inganta rayuwar al’umma.
Taron ya samu halartar manyan Content Creators na Malumfashi da ma na sauran wurare, da kuma dimbin masu amfani da kafafen sada zumunta. Alhamdulillah, an gudanar da taron cikin nasara da armashi.
Muna mika godiya ta musamman da addu’ar fatan alheri ga wadanda s**a gabatar da wannan muhimmin Lecture:
PROF. BALA MUHAMMAD
Department of Mass Communication,
Bayero University Kano.
PROF. SUNUSI IGUDA
Department of Mass Communication,
Bayero University Kano.
Allah Ya saka musu da alheri mai yawa, Ya kara musu ilimi, basira da hikima, Ya kuma sanya wannan aiki ya zama sadaka mai gudana a gare su. Allah Ya amfanar da al’umma da ilimin da s**a koyar. 🤲
Haka kuma, muna mika godiya da jinjina ga dukkan wadanda s**a halarci wannan taro. Kasancewarku da gudummawarku sun kara wa taron armashi da muhimmanci. Allah Ya saka muku da alheri, Ya kuma taimake mu baki daya wajen amfani da Social Media wajen yada alheri, gaskiya da abubuwan da za su amfani al’umma.
A karshe, muna mika godiya ta musamman ga Galadiman Abdulmuminu Center for Learning and Documentation, Malumfashi, bisa wannan kyakkyawan kokari na samar da ilimi da wayar da kan al’umma.
Allah Ya kara daukaka wannan cibiya, Ya albarkaci shugabanninta da ma’aikatanta, Ya kuma sanya ta ci gaba da kasancewa madogara wajen neman ilimi, karatu da ci gaban al’umma.
Alhamdulillah, ilimi shi ne haske, kuma amfani da shi wajen gina al’umma shi ne babban abin alfahari.
daga GALCM