
16/09/2025
Sarkin Zuru ya kai ziyarar jaje ga yan' kasuwar Zuru ya bayar da tallafin Naira ₦250,000 ga kowane Mutum Daya wadanda Gobarar kasuwar ta rutsa da su.
Mai martaba sarkin Zuru Alh Sanusi Mikailu Sami Sami Gomo III a yayin ziyararsa ya bayyana matukar jimaminsa game da wannan masifa da ta afkawa dimbin yan kasuwar tare da kone dukiyoyi masu tarin yawa.
Mai martaba Sarkin Zuru ya bayyana tausayinsa ga wadanda abin ya shafa Allah ya mayar musu da sabon arziki.
Sarkin ya baiwa kowane mai shago da Gobarar ta rutsa da shi Naira dubu ₦250,000 don rage musu radadin wannan babban al'amarin.
Sarkin Zuru ya samu rakiyar mataimakin shugaban karamar hukumar Mulkin Zuru Hon Samaila Abdullah da APC Chairman Zuru Alh Aliyu Abubakar Abiola da jami'an tsaro domin yin jaje ga yan' kasuwar da abin ya shafa.
📸 Abbakar Aleeyu Anache