GCI HAUSA

GCI HAUSA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from GCI HAUSA, Media/News Company, Opposite Green House Mani, Mani.
(1)

Jaridar (Truth Lens Hausa) Jarida ce dake bayyana gaskiyar da a ɓoye ta a ƙarkashin ƙasa, wanda a kasa bayyana ta) Manufar mu shine samar da jagoranci Nagari a inuwar Dimokiradiyya.

19/09/2025

A daren jiya ne, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya kai wa tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Ali Isa Pantami, ziyara a gidansa.

Gwamna Abdullahi Sule Ya Gana da NSA Nuhu Ribadu a  Birnin taraiya Abuja Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. S...
17/09/2025

Gwamna Abdullahi Sule Ya Gana da NSA Nuhu Ribadu a Birnin taraiya Abuja

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, ya gana da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Sha'anin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, a ofishinsa da ke Abuja, domin tattaunawa kan batutuwan tsaro a jihar.

Ganawar ta mayar da hankali kan yadda za a inganta dabarun tsaro da kuma tabbatar da kariya ga rayukan jama’a da dukiyoyinsu a sassa daban-daban na jihar.

A yayin taron, Gwamna Sule ya yi alkawarin ci gaba da yin aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro na tarayya don ganin an shawo kan kalubalen tsaro da ke fuskantar jihar.

Mallam Nuhu Ribadu ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da mara wa Jihar Nasarawa baya wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta tsare tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC Limite...
10/09/2025

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta tsare tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC Limited), Mele Kyari, bisa zargin aikata rashawa da kuma badakalar kuɗi.

Rahotanni sun nuna cewa Kyari ya isa ofishin EFCC da ke Abuja da yammacin Laraba domin amsa tambayoyi. An danganta binciken da ake masa da aikin gyaran matatun mai na dala biliyan $7.2 da aka kaddamar a lokacin shugabancinsa.

Wannan na zuwa ne makonni bayan EFCC ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema, sannan kuma wata kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a dakatar da wasu asusun banki guda huɗu da ake zargin na da alaka da shi.

Ana sa ran hukumar za ta fitar da ƙarin bayani yayin da bincike ke ci gaba.

DA DUMI-DUMI:  Sanata Ahmed Wadada Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a hukumance.
21/08/2025

DA DUMI-DUMI: Sanata Ahmed Wadada Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a hukumance.

YANZU-YANZU: Shugaba Bola Ahmed ya isa birnin Tokyo na kasar Japan Gabannin taron TICAD na 2025, Ambasada Hideo MATSUBAR...
18/08/2025

YANZU-YANZU: Shugaba Bola Ahmed ya isa birnin Tokyo na kasar Japan Gabannin taron TICAD na 2025, Ambasada Hideo MATSUBARA, jakadan Japan mai kula da TICAD ya tarbe shi.

YANZU-YANZU: ‘Yan sanda sun gano bama-bamai a wata gona a jihar BornoJami’an rundunar ‘yan sandan jihar Borno sun gano w...
18/08/2025

YANZU-YANZU: ‘Yan sanda sun gano bama-bamai a wata gona a jihar Borno

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Borno sun gano wani bam da bai tashi ba a wata gona da ke karamar hukumar Dikwa, ta jihar Borno.

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Bauchi A Zaɓen da Ya Gabata na 2023. Air Marshall Baba Sadiq Ya Ziyarci Tsohon Gwamnan jihar S...
16/08/2025

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Bauchi A Zaɓen da Ya Gabata na 2023. Air Marshall Baba Sadiq Ya Ziyarci Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Sen Aminu Waziri Tambuwal Domin Jajanta masa bayan tsare shi da Hukumar EFCC Tayi.

16/08/2025

Yahaya Ladan (Shafele, kakakin Sarkin Keffi) ya koka kan rashin adalcin da ake yi masa a kan filin da ya gada daga iyayensa da kakanninsa.

‎Yahaya Ladan (Shafele kakakin Sarkin Keffi) ya koka da rashin Adalci da ake Yunkurin masa, akan Filinsa daya gada iyaye...
16/08/2025

‎Yahaya Ladan (Shafele kakakin Sarkin Keffi) ya koka da rashin Adalci da ake Yunkurin masa, akan Filinsa daya gada iyaye da kakanni.

‎Malam Yahaya Ladan, Sun mallaki Wannan filin ne a wajen mahaifinsu, wanda daya daga cikin yaron yayansu Mai suna Ibrahim, ya dauki filin ya sayar da wani shashin filin ga wani Inyamuri dake Garin Keffi, Mai suna Victor Inyama.

‎A Cewar Ladan, ya shigar da karar Inyamurin a babbar Kotun High Court 2 dake garin keffi, wanda daga bisani ya sani nasara a Kotun har sau biyu.

‎A yanzu yana zargin Dangoten Keffi da Yunkurin kwace Masa Fili dake Yankin GRA a garin Keffi ta jihar Nasarawa.

‎Wakilin mu ya tuntubi bangaren wanda ake zargi Dangoten Keffi akan jin ta bakinsa, Sai dai ya bayyanawa wakilin mu cewa shi baya hira da Yan jarida, kuma magana na gaban kotu, dan haka ba zaice komi ba

‎Yahaya Ladan, yayi kira ga Mahukunta na Garin Keffi da Jihar Nasarawa akan su shiga cikin wannan lamari domin samar da daidaito.

Dan jarida Abdul Journalist 1  ya bayyana matuƙar girmamawarsa ga fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, bisa yadda...
10/08/2025

Dan jarida Abdul Journalist 1 ya bayyana matuƙar girmamawarsa ga fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, bisa yadda ta bi wasiyyar mahaifinta wajen yin aure bisa tsarin da Musulunci ya tanada.

A cewarsa, Rahama Sadau ta gudanar da auren cikin ladabi da mutunci, ba tare da nuna alfahari ko yin fitsara ba. Ya bayyana wannan mataki nata a matsayin abin koyi ga sauran mata, yana mai yabawa da cewa wannan shi ne auren da ake buƙata a shari’ar Musulunci.

Abdul Journalist ya ƙara da cewa suna yi mata addu’ar Allah ya bata zaman lafiya, da zuri’a ta gari, tare da dorewar farin ciki a sabuwar rayuwarta ta aure.

Matashiya daga Jihar Yobe, ta doke Kasashen Turawa 69 a Gasar Ingilishi Ta DuniyaƊaliba mai shekara 17 daga jihar Yobe, ...
04/08/2025

Matashiya daga Jihar Yobe, ta doke Kasashen Turawa 69 a Gasar Ingilishi Ta Duniya

Ɗaliba mai shekara 17 daga jihar Yobe, Nafisa Abdullah Aminu, ta kafa tarihi a gasar TeenEagle Global Finals 2025 da aka gudanar a birnin London ta ƙasar Birtaniya, inda ta lashe kambun gwarzuwar ɗaliba mafi ƙwarewa a harshen Turanci a duniya.

Nafisa, wadda ta wakilci Najeriya ƙarƙashin Nigerian Tulip International College (NTIC), Yobe, ta doke sama da dalibai 20,000 daga ƙasashe 69, ciki har da waɗanda ke magana da harshen Turanci a matsayin yaren uwa.

Wannan gagarumar nasara ta janyo yabo da farin ciki daga 'yan Najeriya da dama, musamman ganin yadda ɗalibar Najeriya daga arewa maso gabas wuri da ake fama da ƙalubalen ilimi amma ta yi fice a matakin duniya.

Na Fara shakka kan Kwarewar Gwamnatin Tinubu da Masu taimaka masa a bangaren Noma.inji  — Abdul Journalist 1 Wannan rash...
03/08/2025

Na Fara shakka kan Kwarewar Gwamnatin Tinubu da Masu taimaka masa a bangaren Noma.inji — Abdul Journalist 1

Wannan rashin mayar da hankali wajen rage farashin takin Da maganin feshi alama ce na shirin rusa manoman mu na Arewa.

Idan har Gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da gaske take son kawo sauki ga Yan Najeriya, ya kamata ace taki da maganin feshi ya zaftaro kasa.

Ina da imanin matukar Wannan hali da manoman Arewa su shiga ciki zai taka rawa wajen ruguza tattalin arzikin Arewa baki daya.

Ya zama dole Gwamnatin Tinubu ta tashi daga dogon bacci ta dauki matakin kawo sauki ga manoma don samun daidaito akan bangaren noma. Domin shine ginshikin tattalin arziƙin ƙasa inji Abdul

Address

Opposite Green House Mani
Mani

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GCI HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share