HASMAG TV

HASMAG TV “Barka da zuwa shafin HASMAG TV 📺
Shafin Dake kawo muku labaran Jihohin Arewacin Najeriya.
📞Ga Masu Son Tuntuɓarmu Ga Lambar Waya: 09121774270
(1)

Yau Shekaru 5 da Rasuwa: Tarihin Marigayi Sarkin Sudan na Kontagora, Sa’idu NamaskaYau, 9 ga Satumba, 2026, shekaru biya...
09/09/2026

Yau Shekaru 5 da Rasuwa: Tarihin Marigayi Sarkin Sudan na Kontagora, Sa’idu Namaska

Yau, 9 ga Satumba, 2026, shekaru biyar ke nan da rasuwar Marigayi Sarkin Sudan na Kontagora, Alhaji Sa’idu Umaru Namaska (CON), wanda ya rasu a ranar 9 ga Satumba, 2021, yana da shekaru 84.

Marigayi Sa’idu Namaska ya hau karagar Sarkin Sudan na Kontagora a shekarar 1974, inda ya shafe kusan shekaru 47 yana jagorantar masarautar har zuwa rasuwarsa. Wannan ya sanya shi cikin sarakunan da s**a dade suna kan karagar mulki a tarihin Masarautar Kontagora.

A tsawon mulkinsa, an san shi da hakuri, mutunci da kokarin hada kan al’umma, tare da taka rawa wajen zaman lafiya da ci gaban masarautar. A lokacin rasuwarsa, an bayyana shi a matsayin basaraken da ya yi tasiri wajen hada kan al’umma da kuma kula da al’adun masarautar.

Rasuwarsa ta kasance babban gibi ga Masarautar Kontagora, bayan kusan rabin karni da ya shafe a kan karagar sarauta. Shekaru biyar bayan rasuwarsa, har yanzu ana ci gaba da tunawa da shi da kyawawan halayensa da tarihin mulkinsa.

Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa. Amin.

Dame kuke tunada marigayi Maimartaba Sarkin Sudan?

Hasmag TV.

08/09/2026

Shin ina Aka Kwana da Kudaden Ayyukan Karamar Hukumar Mashegu na Sama da Biliyan 3?

Kashi na Daya.

Dukkanin su Sun Taba Rike wani Mukami a Jihar Neja.Shin wani cigaba S**a kawowa yankin nasu?
08/09/2026

Dukkanin su Sun Taba Rike wani Mukami a Jihar Neja.

Shin wani cigaba S**a kawowa yankin nasu?

07/09/2026

Mutanen mashegu ankai fagen da dole Mutum ya ajiye mota ya koma hawan mashin Saboda Tsoron Kar ayi garkuwa Dashi.

Mutanen karamar hukumar ba Solar ko Friza suke bukata ba,Tsaro Shine babban Matsalar Al'ummar Mashegu.

Karamar Hukumar Mashegu na Samun Miliyan 10 ne kacal a wata Domin gudanar da Ayyukan Karamar Hukumar.

Cewar Mataimakin Shugaban Ma'aikatar karamar hukumar mashegu a jihar Neja.

Masu son Zantawa damu su tuntubemu a 08145393645

HASMAG TV

07/09/2026

Gwamnatin Bago na tabbatar da cewa ainihin shugabanci ana auna shi ne da ci gaban da ake gani a zahiri, ba da alkawurika ba

Gwamnan Jihar Neja, Hon. Mohammed Umaru Bago, ya amince da naɗin wasu sabbin kwamishinoni da masu ba shi shawara a fanni...
07/09/2026

Gwamnan Jihar Neja, Hon. Mohammed Umaru Bago, ya amince da naɗin wasu sabbin kwamishinoni da masu ba shi shawara a fannin siyasa, domin ƙara ƙarfafa harkokin gudanar da mulki da inganta ayyukan gwamnati a jihar.

Sabbin naɗe-naɗen, waɗanda ke ƙarƙashin sahalewar Majalisar Dokokin Jihar Neja, sun haɗa da mutum shida da aka naɗa a matsayin Kwamishinoni-Designate,Sun hada da:-

Hon. Lucky Barau – Ƙaramar Hukumar Gurara
Hon. Isah Wakili – Ƙaramar Hukumar Bosso
Dr. Isah Adamu – Ƙaramar Hukumar Kontagora
Hon. Emmanuel Alamu – Ƙaramar Hukumar Magama
Hon. Shuaibu Saidu Kaboji – Ƙaramar Hukumar Mashegu
Mohammed Danladi Garba – Ƙaramar Hukumar Borgu

Haka kuma, Gwamna Bago ya amince da naɗin wasu mutane a matsayin masu ba shi shawara kan harkokin siyasa, inda Alhaji Nma Kolo ya zama Babban Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa (Chief Political Adviser).
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da:

Yahaya Emilugi – Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Zone A.
Yusuf Tagwai – Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Zone B.
Salman Yusuf – Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Zone C.

HASMAG TV

Kungiyar KBM na Cigaba da Ganawa da Al’umma Domin Tabbatar Da Nasarar Gwamna Bago Da Mataimakin sa Yakubu  Garba.Ƙungiya...
07/09/2026

Kungiyar KBM na Cigaba da Ganawa da Al’umma Domin Tabbatar Da Nasarar Gwamna Bago Da Mataimakin sa Yakubu Garba.

Ƙungiyar mai suna King Boys Movement, ta ziyarci gundumomin Kodo, Shata da Garatu da ke ƙaramar hukumar Bosso, inda ta gana da mata, matasa da dattawa, tare da sauraron buƙatun al’umma da kuma tallafa wa wasu daga cikin mata masu sana'in dogaro da kai.

KBM ta bayyana cewa za ta ci gaba da kusantar al’umma, sauraron ra’ayoyinsu da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Haka kuma, tana ci gaba da isar da saƙon Bago/Yakubu 2027 ga al’umma, tare da neman goyon bayansu domin tabbatar da ci gaba da manufofin ci gaban Jihar Neja da gwamnatin ta sa ɗanba.

Allah yayi Zainab Zee Diamond na cikin shirin Labarina Rasuwa bayan Fama Da Rashin LafiyaAllah ya jikanta
07/09/2026

Allah yayi Zainab Zee Diamond na cikin shirin Labarina Rasuwa bayan Fama Da Rashin Lafiya

Allah ya jikanta

06/09/2026

Shirin Daga T**i Tare da Salamatu Alhassan Musa.

Ku fada Mana Shin me ake cewa “Toilet” da Hausa a Comment Section.

Hon. Barr. Lawal Yusuf, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kontagora, ya kawo kamfanin gine-ginen tituna TRIACTA domin ƙaddamar da...
06/09/2026

Hon. Barr. Lawal Yusuf, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kontagora, ya kawo kamfanin gine-ginen tituna TRIACTA domin ƙaddamar da aikin gyaran T**in Makabarta Gabas.

A ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026, ake sa ran za a fara aikin titin, yayin da a halin yanzu ma’aikata ke gudanar da aikin sharewa da baje ƙasan hanyar domin sauƙaƙa zirga-zirga kafin a fara babban aikin.

HASMAG TV

Address

S Pawa Plaza, Sule Barau Street Opposite Central Primary School Kontagora
Mani

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HASMAG TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share