14/09/2025
Miji ya caka wa matarsa yawan wuka...
sannan ya É—auki jaririyarsu ya faÉ—o da ita daga bene na biyar...
Wani abu da ba za a iya gaskatawa ba, amma ya faru da gaske a garin Zefta, yankin Gharbia... cikin firgici daga makwabta da girgiza daga al'umma...
Mijin, wanda yake fama da matsanancin tabin hankali, ya samu sabani mai tsanani da matarsa wanda ya ƙare da mummunar kisa...
Ba wai kawai ya sare ta da wuka ba, har ya É—auki 'yarsu jaririya, wacce bata kai watanni takwas ba a duniya, ya rungume ta...
sannan ya fado da ita daga tagar bene na biyar, wani lamari da ya karya zukata...
Mijin ya rasu nan take, tare da jaririyar da bata san komai ba daga rayuwa...
Amma matar, an garzaya da ita asibiti a mawuyacin hali, tsakanin rai da mutuwa...
Binciken farko ya nuna cewa mijin yana fama da matsanancin damuwa da halin yau da kullum, kuma wataƙila ya gano kwanan nan cewa yana da wata cuta mai tsanani, wanda hakan ya ƙara dagula lissafinsa da juyar da hankalinsa...
Lamarin ya girgiza al'umma a Masar baki ɗaya, ba wai saboda ƙiyayarsa kawai ba, amma domin yana nuna yadda ciwon rai da na zuciya zai iya haifar da masifa da ta shafi kowa...
Abin da ya faru ba wai kawai kisan gida ba ne...
wata irin ƙara ce ta ciwon zuciya da ke fitowa daga al’umma mai rauni...
Miji ya sare matarsa, ya É—auki jaririyarsu, ya faÉ—o da ita daga bene na biyar! Wani lamari mai É—aci, amma ba ya zuwa haka kawai...
Wa ya sani me yake faruwa a ransa? Me ya kai shi ga wannan matsayi? Wataƙila yana fama da wani irin baƙin ciki da babu wanda ya lura da shi... wataƙila yana buƙatar ya ji kalmar “Ina tare da kai,” maimakon zargi da tsangwama...
Wannan mutanen ba nesa suke da mu ba... kowa a cikin mu na iya zama haka...
Abokin zama... mata... mijinki... É—an uwa...
Wanda ya yi shiru na iya zama yana ƙara...
Wanda kuke ganin yana dariya, na iya kasancewa yana kuka daga ciki, kuma baya samun kafadar da zai jingina da ita...
Ku tambayi juna ya kuke ji, 'yan uwa... ku tausaya wa juna... kayi following Hambali Hamisu
Kada mu ci gaba da zama masu ƙyama da kalmomi... kada mu ci gaba da hayaniya saboda ƙaramar magana...
Kada mu tsaya jiran kuskuren wasu don mu rufe su da tsawa...
Kalmomi masu daɗi, runguma ta gaske, ko ma tambaya irin ta “Ya kake?” daga zuciya...
na iya zama dalilin da zai hana wani durƙushewa, kuma ya ceci jaririya daga mutuwa...
Ba lallai ne mu zama mutane cikakkaku ba...
Amma Na rantse da Allah, abin da muke buƙata kawai shi ne mu zama mutane masu jin kan junan mu