14/11/2025
NAAES NHQ TA KALLO LABARIN TALLAFIN KARATU DA KE YADAWA A DANDALIN SADA ZUMUNTA
Shugabannin Kungiyar Daliban Masarautar Agaie ta Kasa (NAAES NHQ) sun bayyana damuwa kan wani labarin da ke yawo a dandalin sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa an bai wa NAAES NHQ tallafin karatu daga ADG. Sanarwar ta ɗauki tambarin ƙungiyar, lamarin da ya jawo ruɗani da tambayoyi daga mambobi, shugabanni, da jama’a baki ɗaya.
Kungiyar ta tabbatar da cewa bata karɓi kowace irin takarda, saƙo, ko sanarwar hukuma daga ADG ko wani wakilinta dangane da wannan tallafi ba. Haka kuma, shugabannin NAAES NHQ ba su san asalinsa, manufarsa, ko wanda ya wallafa shi ba.
A matsayin ƙungiya mai mutunta gaskiya da adalci, NAAES NHQ ta jaddada cewa duk wani saƙo da ake yadawa da sunanta dole ne ya kasance tabbatacce, na gaskiya, kuma an amince da shi ta hanyar hukuma.
Saboda haka, NAAES NHQ na kira ga Shettima Agaie Foundation (SAF) da ta fito fili ta yi bayani kan asalin sanarwar, tushenta, da kuma ko an amince da ita daga hukumarta. Wannan mataki zai taimaka wajen kare martabar ɓangarori biyu da kuma kaucewa yaɗa bayanan da ba su tabbata ba.
Bugu da ƙari, NAAES NHQ ta sanar da jama’a cewa ba za ta amince ko ta yada kowanne tallafin karatu ko shirin ilimi ba sai wanda aka tabbatar da shi ta hanyar hukuma kuma an tsara shi tare da jagorancin NAAES National Executive Council. Wannan tsari na da nufin tabbatar da cewa dalibanmu suna samun sahihan damar ilimi ba zamba ba.
Hankali: Duk wani bayani game da tallafin karatu daga ADG da za a wallafa a dandalin sada zumunta ya k**ata ya samu tabbaci daga NAAES NHQ kafin a yada shi.