22/07/2022
ATIKU YA KOKA KAN YAWAN KATSEWAR BABBAR TASHAR LANTARKI TA KASA, YA YI ALKAWARIN KAFA ASUSUN LAMUNIN SAMAR DA KAYAN AIKI (IDF)
Dan Takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP a shekarar 2023 Alhaji Atiku Abubakar ya koka game da yawan lalacewar babbar tashar Samar da lantarki ta kasa da kuma illar hakan ga kasa, yana Mai cewa wannan shi ne karo na shida cikin wannan shekara da hakan ke faruwa.
A Wani Sako da aka wallafa a shafin sa na Twitter, Wazirin Adamawa ya zayyana muhimmancin bangaren lantarki da kuma illar da rashin wutar ke haifarwa ga sauran sassan tatttalin arziki. Saboda daukar wannan bangare da muhimmancin gaske, Atiku ya kudiri aniyar Samar da abinda ya kira, kirkirar hanyar Samar da kudaden aiwatar da gine-gine da sauran kayan aiki da zasu share fagen kwaskwarima ga tsarin kasafta kudade, da fannin shari'a da dokoki domin bunkasa harkokin zuba jari a bangaren lantarki da sauran fannoni.
Haka kuma, ya yi alkawarin Samar da tsari na tallafawa da rangwame kan haraji ga bangarori masu zaman kan su don kafa asusun lamuni kan ayyuka, inda za a fara da akalla jarin Dala miliyan dubu 20 da nufin farauto kudade Daga gida da Waje don gudanar da manyan ayyuka a dukkan bangarorin tatttalin arziki.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya nuna mutukar damuwar sa kan yadda za a farfado da tatttalin arziki kasa, Inda yace zai yi aiki domin kafa wata hukuma ta bada tabbaci kan lamuni domin aiki tare da wancan asusun, don rage yawan hadarin da ka iya aukuwa da nufin karfafa gwiwar masu zuba jari.
AbdulRasheeth Shehu
Mataimaki na Musamman ga Mai girma Atiku Abubakar Kan Kafofin Watsa Labarai
21 ga Yuli, 2022.