12/07/2024
Magani Daga Tsirrai
Ku ziyarci shafin Salisu A Farouk domin samun ilimin da ya shafi noma da kiwo da kuma magunguna.
Kamar yadda na ke ta ƙoƙarin baje-kolin magunguna daga tsirrai, yau ma na zo maku da wani magani na cutar da ake cewa ' Amosani' , wannan maganin gaskiya mai inganci ne, kuma Insha-Allahu za a dace, mu kalli waɗannan abubuwan :
—Mahaɗi (Ingredients)
1. A nemo kanumfari.
2. A nemo man-shanu.
—Yadda Za a Haɗa Maganin (Method Of Preparation)
1. A murza wannan kanumfarin a maburgi (wani abun niƙa ne na gargajiya) ko kuma a niƙashi ta kowacce hanya da zai yi laushi sosai ya bada gari.
2. Sai a ɗauko wannan man-shanun a cakuɗasu, a tonasu sosai, su haɗu kamar man-shafawa.
—Yadda Za Ai Aiki Da Shi (Method Of Application)
1. Mutum zai yi aski, ko ƙwalkwabo ko kuma sai-saye wanda za a aske sosai, yanda idan an saka maganin zai isa har kan fatarka ta kanka.
2. Kullum da daddare sai ka ɗebi wannan haɗin na ka ka shafa a kanka, ka goga sosai, idan ka shafe kanka sai ka sami hula ka saka a kanka, gudun ka da maiƙon man-shanun ya ɓata maka kai.
3. Idan gari ya waye, sai ka samu ruwan zafi, ka samu klin, sai ka wanke kanka da su, ka yi haka kamar sau uku, Idan kuma ya tsananta ka yi sau bakwai, Insha-Allahu za a dace.
—Abinda Ya ke karewa (Cure Of Medicine)
1. Zai maganin amosanin ka.
2. Zai maganin amosanin da ya sauko kan idonka ya ke maka ƙaiƙai.
3. Zai maganin amosanin da ya sauko kan haƙoranka ya ke haifar maka da zubar jini daga bakinka.
4. Zai ƙarawa idanuwanka ƙarfin gani.
Dan Allah a gwada ! Na gode.
© Salisu A Farouk
Diploma In Agro-forestry Technology.
Chief Executive Officer Saf Garden Online School And Agricultural services