27/09/2026
LABARI MAI DAƊI: SOJOJIN OPERATION FANSAN YAMMA SUN CETO MUTANE 31 DA AKA SACE
Rundunar Sojin Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, ta ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi.
A Katsina, an ceto mutane 10, ciki har da wani jariri, bayan wani samame da bin sawun ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Funtua.
A Kebbi kuwa, sojojin sun ceto wasu mutane 21 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Kangiwa, inda daga bisani aka mayar da su ga iyalansu.
Haka kuma, sojojin sun kashe wasu ’yan ta’adda biyu, ciki har da wanda ake zargin jagoran ƙungiyar ne, Abbah Alhassan, tare da k**a wasu mutane biyu da ake zargi da hannu cikin ayyukan ta’addanci.
Wannan nasara na ƙara ƙarfafa fata na samun zaman lafiya a yankunan Arewa maso Yamma.
Muna yaba wa jami’an Operation FANSAN YAMMA bisa jajircewa da sadaukarwarsu wajen kare rayukan al’umma.