28/11/2025
DA ALAMA HAKAN YA TEMAKA WAJEN SAMAR DA TSARO....
Wani mai sharhi akan harkokin tsaro a Africa shine naga ya sanar da cewa ....
Wata majiya ta sirri wacce ke da masaniya akan yarjejeniyar soja da aka sanya hannu tsakanin kasar Amurka da Nigeria, an sanar dashi cewa an bawa Amurka damar kai farmaki ta amfani da jiragen sama marasa matuki wato (UAV) zuwa kan yan ta'adda dake ayyukan taadanci a Nigeria...
Yarjejeniyar ta amincewa sojojin Amurka suyi amfani da sansaninsu dake kasar Ghana su kai farmaki kai tsaye ga yan ta'adda da masu halaka mutane dake ayyuka a Nigeria...
Sannan zaa dinga musanyar bayanai kai tsaye tsakanin sojojin Nigeria da sojojin Amurka domin tallafawa juna da bayanan sirrin da zasu temaka wajen shawo kan matsalolin tsaro dake addabar yankin Arewa...
Shi dai masanin harkokin tsaro maisuna BRANT ya rubuta cewa meyiyuwa anan gaba zaa samar da wata haɗakar sojojin Amurka da Nigeria da zasu yi amfani da wani yanki na jihar Niger dake Ka'inji domin tafiyar da ayyukan kai hare hare ga yan ta'adda masu halaka mutane...
A shafin Twitter na hango wannan bayanin na masanin harkokin tsaro BRANT har ma nayi screenshot saboda aje hujja, zan saka a comment section...