Nigerwatch Hausa

Directions

Nigerwatch Hausa Labarai Cikin Hausa

05/10/2026

Kanun Labarai Daga Bakin Rukaiyat Jalingo

゚viralシ ゚ Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Atiku Abubakar

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir B...
03/10/2026

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, murnar cika shekaru 45 da haihuwa.

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Asabar, cewa Tinubu ya bayyana Bichi, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Bichi a Jihar Kano, a matsayin ɗan majalisa mai ƙwazo, basira da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukan majalisa da ci gaban ƙasa.

Shugaban Ƙasar ya yaba da rawar da Bichi ke takawa a matsayinsa na shugaban ɗaya daga cikin muhimman kwamitocin Majalisar Wakilai, musamman wajen jagorantar nazari da tantancewa da kuma amincewa da kasafin kuɗin ƙasa na shekara-shekara. Ya kuma yaba da wakilcin da yake yi wa al’ummarsa da ayyukan da ya ce sun shafi ilimi, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafa matasa.

Bola Tinubu ya kuma bayyana cewa Bichi ya bambanta kansa tun bayan zaɓensa na farko zuwa Majalisar Wakilai a shekarar 2019, inda ya taɓa jagorantar Kwamitin Ayyuka a Majalisa ta Tara, kafin ya zama Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi a Majalisa ta Goma. Ya roƙe shi da ya ƙara mayar da hankali wajen yi wa al’ummarsa da ƙasa hidima, tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, hikima da ƙarfi.

30/09/2026

Kanun Labarai Daga Bakin Rukaiyat Jalingo

゚viralシ ゚ Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

21/09/2026

Kanun Labarai Daga Bakin Rukaiyat Jalingo

゚viralシ ゚ Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

19/09/2026

Jami'an da civil defence waɗanda aka dakatar dake da alaƙa da mutuwar Yan zinari s Jihar Neja sune....

1. QC Station Guard, SC Usman Isah Ndamaka

2. Station Guard, ASCI Hassan Mohammed

3. Station Guard, CCA Bala Mohammed

4. Arresting Officer/O/C Investigation, CSC Oluwadare Sunday

5. Arresting Officer, DCC Obafemi Elvis

6. Arresting Officer, CSC Annas Sh*tto Lamino

7. HOD INT/INV, DCC Philip Ajayi

8. O/C Legal, ACC Barr. Stephen Tsado

9. Day/Night Duty Officer, ASCI Alhassan Mohammed

10. Guard Duty, IC Abdullahi Sale

11. Guard Duty, IC Mohammed Sonfada

12. Guard Duty, CAI Liman Abubakar

13. Guard Duty, CAI Bala Usman

14. Guard Duty, IC Mohammed Jiya

15. Guard Duty, DSC Isah Suleiman

16. Guard Duty, CAI Ahmed Wushishi

17. Guard Duty, IC Sale Adamu

18. Guard Duty, IC Haruna Mohammed

19. Guard Duty, ASCI Aliyu Sallah

20. Guard Duty, CAI Isah Sanusi

Dakatarwar ya hada da Kwamandan Rundunar na Jiha.

14/09/2026

Sharhi daga bakin Salis Sani Voice Salis Sani Voice

Ku biyo mu daki daki ku ji me Atiku Abubakar ke tafe dashi akan dawo da tallafin man fetur

11/09/2026

Kanun Labarai Daga Bakin Rukaiyat Jalingo

゚viralシ ゚ embassy Nigeria mission

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027Ƙungiyar "Charismatic Bishops Conference of Nigeria" (CBCN) ta bayya...
10/09/2026

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

Ƙungiyar "Charismatic Bishops Conference of Nigeria" (CBCN) ta bayyana goyon bayan ta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.

Shugaban CBCN, Archbishop Prof. Leonard Bature Kawas, shi ne ya bayyana matsayar ƙungiyar a ranar Laraba a Abuja, a lokacin da ake gudanar da babban taron Synod na 2026 na CBCN da ICCABA a Majami'ar Kiristoci ta Ƙasa.

Kawas ya ce ƙungiyar ta yi nazari kan ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da bayyana shirin ta na ci gaba da mara wa shugaban ƙasar baya ta hanyar addu’a, bayar da shawarwari da kuma wayar da kai.

Ya ce: “Mun goyi bayan sa a yanzu. Mun goyi bayan sa yau, za mu goyi bayan sa gobe, kuma za mu ci gaba da goya masa baya muddin yana son kasancewa shugaban ƙasar mu.”

Ya ƙara da cewa: “Wannan gida ya amince da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.”

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci shugabannin addini da su yi amfani da tasirin su wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da kyakkyawar mu’amala tsakanin al’umma gabanin zaɓen 2027.

Ya ce: “Ci gaba da haɗa kan wannan ƙasa na buƙatar fiye da matakan gwamnati. Yana buƙatar jagoranci nagari daga dukkan ɓangarorin al’umma, ciki har da jagorancin addini."

Idris ya yi gargaɗi kan yunƙurin nuna matsalolin tsaron Nijeriya a matsayin yaƙin addini, yana mai cewa ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun kai wa ’yan Nijeriya hare-hare ba tare da la’akari da addinin su ko asalin su ba.

“Kada a bari wani zaɓe ya sa Kirista ya juya wa Musulmi baya, ko Musulmi ya juya wa Kirista baya, ko Arewa ta juya wa Kudu baya, ko wata ƙabila ta juya wa wata baya. Nijeriya tamu ce baki ɗaya,” inji shi.

Da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Tinubu, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya yaba wa ma'abota cocin kan gudunmawar su ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da kira da a samu ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin addini.

Ya ce: “Gwamnati tana buƙatar gudunmawar Kiristoci wajen kyautata ɗabi’a da tarbiyyar al’umma, yayin da Kiristoci suke buƙatar yanayin da zai ba su damar gudanar da ayyukan su da kyau. Fiye da komai, Nijeriya tana buƙatar mu yi aiki tare domin amfanin kowa.”

03/09/2026

Ta’aziyar Rasuwar Shuguban Kidaya ta kasa, Alhaji Aminu Yusuf.

Address

Minna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigerwatch Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share