27/10/2025
ALLAHU AKBAR: Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Zama Malami Mafi Yawan Dalibai a Fadin Afirka — In Ji Binciken Masana
Wani rahoton bincike daga masana addini da ilimi a nahiyar Afirka ya tabbatar da cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne malami guda da ke da yawan dalibai da mahaddatan Al-Kur’ani fiye da kowane malami a yankin.
Masana sun bayyana cewa, wannan nasara ta Sheikh Dahiru Bauchi ta samo asali ne daga tsawon shekaru na hidima ga ilimin addini, karatun Al-Kur’ani, da kuma wa’azin da ya shimfiɗa ko’ina cikin Afirka.
Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance jigo a harkar ilimi da karantarwa, kuma ya kafa makarantu masu tarin yawa da s**a samar da dubban hafizai da malamai da ke yada ilimi a sassa daban-daban na duniya.
A yayin da rahoton ya ke yawo a kafafen sada zumunta, mutane da dama sun rika bayyana fatan alheri da addu’o’in samun karin lafiya, tsawon rai da ƙarfafa masa gwiwa wajen ci gaba da hidima ga addini.
“Allah Ya ƙara masa lafiya, Ya tsawaita rayuwarsa cikin albarka, Ya ba shi ikon ci gaba da jagorantar al’umma bisa tafarkin Al-Kur’ani da Sunnah.”