28/09/2025
Daga ƙarshe dai Yakubu Muhammad Salisu ya bayyana abunda ya faru da shi a wani wallafa da ya yi a kafar Facebook:
Waƙa a bakin mai ita.....
Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai wadda ya ƙaddari rayuwarmu zuwa wannan rana. Alhamdulillah alaa kulli haalin.
Ina wannan rubutun ne ba don komai ba sai don nayi bayani ma mutane ainihin abinda ya faru na jarabawar da ta same ni a kwanan nan daga ranar talata zuwa jiya Asabat tsakanina da mai martaba Sarkin Misau Alh. Ahmed Sulaiman MNI.
Bidiyona wadda nayi rashin kyautawa na zagin Mai martaba, wadda wannan video tsoho ne tsawon shekara biyu(shekarar 2023) da s**a wuce a garin da nake makaranta wani Abokina ya ɗauke ni. Ina so jama'a su sani cewa a wancan lokacin iyayena, da illaahirin ƴan uwana sun min babu daɗi sun hukunta ni tare da nuna min kuskurena, ni kuma nayi alkawarin In shaa Allah ba zan sake zagin wani bama ballantana mutum k**ar Sarkin gari irin Misau. A babin adalci, k**ar yadda idan mutum ya kai ɗinki Tela zai gwada shi, idan ya gwada zai iya samun hanu ko wani ɓangare na jikin mutum ya ƙara tsawo ko girma, haka nima duk ƙiyayyan da mutum zai min yak**ata ya min adalci wajan ganin ɗabi'una sun chanza daga marasa kyau zuwa kyawawa a shekara biyun nan. Amma mutane sai suke tunanin akasin hakan suna zagi na suna rage min.
Ranar talata da ta wuce saɓani ya shiga tsakanin wasu Abokaina da wadda ya min wannan video shekaru 2 biyu baya, sabida kawai ban goyi bayansa ba sai yaji haushina. Sai yayi amfani da wannan video wadda wallahi na manta da shi ma kuma ban taɓa tunanin zai min irin wannan abin ba, don kawai yaga na shiga ƙunci, kuma na shiga ƙuncin shi kuma ya ji daɗi.
Ya garzaya fadan Mai martaba da wannan video ya nuna masa cewar a ɗauki mataki a kaina.
Kwatsam da safiya ranar laraba zamu tafi gona ni da mahaifina ko karyawa ban yi ba, aka zo aka ɗauke ni daga gida zuwa fadar Mai martaba, aka min dukan fitan hankali na tsawon minti 45 zuwa awa ɗaya wadda tun ina basu haƙuri har numfashina ya fara sama-sama na kasa kuka daga bisani sai aka ɗauke ni zuwa police station aka kulle ni. Idan da na mutu a lokacin da suke min jungle justice yaya kenan oho🥲🥲🥲.
A tunanina na yaro ƙarami, ina ganin k**ar da zai fi dacewa Sarki ya saka a ɗauko ni daga ni har Babana a faɗa masa abinda nayi, kuma Sarki ya sanya a mini hukunci a gabansa, kuma ya min faɗa ya min babu daɗi ni kuma zan bada haƙuri tare da yin da na sanin abinda nayi a matsayina na mai tarbiyyar musulunci. Amma an samu akasi hakan bai yiwu ba.
Daga ƙarshe ina yi ma kowa fatan alkhairi. Wadda suke kan tunanin hukuncin yayi na gode muku. Wadda kuma suke ganin hukuncin da na faɗa shine daidai suma Na gode musu.
Allah ya haɗa mu da Abokai nagari, Allah ka hana mu yin annamimanci da zagon ƙasa. Allah ya ƙara albarka a garin Misau da mutanen cikinta. Bissalaaam.
Yakubu Muhammad Salisu (Mu'allim)