13/06/2026
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya sanar da yin afuwa ga fursunoni 97 da s**a cancanta a Gidan Gyaran Hali na Tsaro Matsakaici da ke Kaduna, a wani bangare na bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2026.
Gwamnan ya ce matakin ya nuna ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, gyaran hali da kuma sake ba wa waɗanda s**a gyaru damar komawa cikin al’umma su ci gaba da rayuwa cikin mutunci.
Uba Sani ya kuma ba da umarnin gaggauta kai kayan magunguna da kuma motar aiki zuwa cibiyar domin inganta kula da lafiyar waɗanda ke tsare da kuma sauƙaƙa gudanar da ayyukan gidan gyaran halin.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su ƙarfafa tsarin gyaran hali da sake tsugunar da waɗanda s**a sauya halayensu cikin al’umma.