23/11/2025
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta bayyana cewa jami’anta biyar sun rasa rayukansu, yayin da biyu s**a ji rauni a wani mummunan hari da aka kai wa tawagar jami’an tsaro yayin sintiri a kauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Darazo.
Wannan lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 22 ga watan Nuwamba, na shekarar 2025, da misalin ƙarfe 12:40 na rana, bayan samun sahihan bayanan sirri daga wani mai ba da gudummawa, wanda ya sanar da cewa an yi wa tawagar jami’an tsaron hadin gwiwa kwanton-bauna.
Jami’an da harin Ya rutsa da su sun haɗa da na rundunar kai daukin gaggawa ta Rapid Response Squad (RRS), da jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma na Mopol wato Mobile Police 10 PMF, da rundunar yaki da garkuwa da mutane wato Anti-Kidnapping Unit (AKU), da kuma jami'an tsaron farin kaya wato State Intelligence Department (SID), waɗanda ke gudanar da sintirin samar da tsaro da rage rikicin manoma da makiyaya a yankin.
A cewar sanarwa daga kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi CSP Mohammed Ahmed Wakil, wasu matasa ne da ba a tantance ko su waye ba ne s**a kai harin, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’ai biyar da suke hada da DSP Ahmad Muhammad (SID), ASP Mustapha Muhammad (10 PMF), Inspector Amarhel Yunusa (10 PMF), Inspector Idris Ahmed (10 PMF), da Corporal Isah Muazu (AKU)
Haka kuma, jami’ai biyu sun samu rauni da s**a hada da Inspector Isah Musa (SID) da Inspector Yusuf Gambo (SID).
Daga samun rahoton harin ne, Baturen dan sanda na Darazo, SP Auwalu Ilu, ya jagoranci ƙarin jami’ai zuwa wujen domin ceto waɗanda s**a jikkata da kuma kwashe gawarwakin waɗanda s**a rasu zuwa Asibitin Darazo.
Rundunar ta ce tana cigaba da ƙoƙarin gano da kuma k**a waɗanda s**a aikata wannan ta’asa, domin tabbatar da an fuskantar da su hukunci.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ziyarci wurin domin duba yanayin lamarin tare da jajanta wa iyalan jami’an da s**a rasa rayukansu.
Ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta gajiya ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.