05/05/2024
An yi takwara wa mahaifin Annabi Muhammadu (SAW) a jihar Bauchi..
--------------
Daya daga cikin matasan malamai a jihar Bauchi AMB Sheik Nasir Sheik Ado Musa Tafawa-Balewa Bauchi ne ya sanya sunan mahaifin Annabi Muhammadu SAW a matsayin takwara gare shi.
Shehin malamin ya ce koda a baya iyayen mu suna sanya wannan suna ne don faranta rai da samun Albarkan mahaifin Annabi Muhammadu Sayyidina Abdullahi.
Kuma a yanzu ina shawartan dukkan masoyan Annabi Muhammadu SAW su ci gaba da dabbaga wannan aiki na sanya sunan mahaifan sa Sayyiduna Abdullahi da Sayyid Amina don faranta ran ɗan su Annabin Rahama (saw).