
24/05/2025
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU, ta yi gargaɗin sake tafiya yajin aiki matuƙar gwamnatin tarayya ta gaza cika dukkan sharuɗɗan yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 2009.
Yayin wani taron manema labarai jiya Juma'a a Abuja, shugaban ASUU na kasa, Dr. Chris Piwuna, ya zargi gwamnatin da nuna halin ko-in-kula game da al’amuran da s**a shafi jami’o’in Najeriya.
Ya ce akwai muhimman batutuwa guda tara da har yanzu ba a warware su ba, ciki har da tsaikon da ya biyo bayan kokarin sake duba yarjejeniyar tun daga shekarar 2017 da kuma dakatar da albashin malaman da s**a shiga yajin aiki a 2022.
Ya kuma yi watsi da ci gaba da amfani da tsarin biyan albashi na IPPIS, wanda ASUU ke ganin ya saɓawa tsarin gudanar da harkokin ilimi na jami’o’i, tare da barazana ga yancin kai da tsarin tafiyar da jami’o’i yadda ya kamata.