Mubi World News

Mubi World News Mubi News, World 🌎 News. Including 🙌
1. Hard News (Politics, Sport etc
2. Soft News (Entertainment,

A yanzu, fiye da kasashe 150 cikin 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ne s**a amince da kasar Falasdinawa a mats...
21/09/2025

A yanzu, fiye da kasashe 150 cikin 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ne s**a amince da kasar Falasdinawa a matsayin mai 'yanci.

Ƙarin bayani: https://bbc.in/47Z2IzD

Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ya tabbatar cewa ƙasar ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yanci daga yau L...
21/09/2025

Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ya tabbatar cewa ƙasar ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yanci daga yau Lahadi.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/47PkFR3 Alhamdulillah

Kamfanin Dangote Zai Fara Dakon Man Fetur Kyauta a Ranar Litinin, Ya Rage Farashin zuwa N841/LitaKamfanin matatar mai na...
12/09/2025

Kamfanin Dangote Zai Fara Dakon Man Fetur Kyauta a Ranar Litinin, Ya Rage Farashin zuwa N841/Lita

Kamfanin matatar mai na Dangote zai fara dakon man fetur kyauta daga ranar Litinin mai zuwa, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ya kuma rage farashin lita daya na man fetur zuwa naira 841, domin rage radadin hauhawar farashin kayayyaki ga 'yan Najeriya.

Wannan shiri na raba mai kyauta ana sa ran zai taimaka wajen saukaka matsin tattalin arziki ga jama'a, musamman masu ƙaramin karfi. Wannan cigaba ya kara jaddada rawar da kamfanin Dangote ke takawa wajen tallafawa al’umma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sabuwar Doka Gomna Fintiri Zai Iya Tube Duk Basaraken da Ba shi da Lafiya..Majalisar dokokin jihar Adamawa, ta ba wa gwa...
12/09/2025

Sabuwar Doka Gomna Fintiri Zai Iya Tube Duk Basaraken da Ba shi da Lafiya..

Majalisar dokokin jihar Adamawa, ta ba wa gwamna damar maye gurbin duk wani basaraken da ba shi da cikakkiyar lafiya.

Dokar ta amince wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ya nada Yarima ko kuma wani daga cikin jinin masarautar a matsayin sarki na riko har zuwa lokacin da basaraken zai samu lafiyar gudanar da sarauta.

Ko kun san sai yanzu ƙasar Ethiopia ta shiga shekarar 2018?Kasar da ke Gabashin Afirka na bin kalandar da ta bambanta da...
11/09/2025

Ko kun san sai yanzu ƙasar Ethiopia ta shiga shekarar 2018?

Kasar da ke Gabashin Afirka na bin kalandar da ta bambanta da wadda mafi yawan ƙasashen duniya ke bi, ga kuma dalilin hakan.

😂

Ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen ya ji rauni ne a ƙafarsa a wasan Najeriya da Rwanda ranar Asabar.Likitan tawagar Super...
07/09/2025

Ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen ya ji rauni ne a ƙafarsa a wasan Najeriya da Rwanda ranar Asabar.

Likitan tawagar Super Eagles ya tabbatar cewa Osimhen ba ya jin daÉ—i a halin yanzu, kuma bai yi tafiya tare da sauraun Æ´an wasan zuwa Afirka ta Kudu ba.

JOB ALERT 💥💥💥NDLEA recruitment application portal to open on 20th September 2025🙌Stay tuned to this platform for updates...
06/09/2025

JOB ALERT 💥💥💥

NDLEA recruitment application portal to open on 20th September 2025🙌

Stay tuned to this platform for updates🙌

06/09/2025
Ayyukan mazaɓu na ƴanmajalisa tamkar fashi ne da rana tsaka - ObasanjoKarin bayani - https://bbc.in/481EGDT
04/09/2025

Ayyukan mazaɓu na ƴanmajalisa tamkar fashi ne da rana tsaka - Obasanjo

Karin bayani - https://bbc.in/481EGDT

Dan wasan na Tottenham, Djed Spence ne zai zama ɗan wasa Musulmi na farko da zai buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar Ingila t...
04/09/2025

Dan wasan na Tottenham, Djed Spence ne zai zama ɗan wasa Musulmi na farko da zai buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar Ingila ta maza cikin sama da shekaru 150.

Spence ya ce yana fatan zama abin koyi ga masu tasowa da kuma fatan kafa tarihi a ƙwallon ƙafa a Ingila. Inji hausa

Shahararren ’dan ta’adda, Ado Aleru, ya kashe mayakansa bakwai a Zamfara bisa zarginsu da cin amana. Rahotanni sun nuna ...
04/09/2025

Shahararren ’dan ta’adda, Ado Aleru, ya kashe mayakansa bakwai a Zamfara bisa zarginsu da cin amana.

Rahotanni sun nuna cewa kashe-kashe sun faru a Takulawa, Turba, Bamamu da dajin Yamma, bayan da Aleru ya zarge su da aikata satar mutane ba tare da izini ba a kan hanyar Gusau – Yankara, abin da ya ce yana barazana ga iyakokinsa tare da jawo hankalin jami’an tsaro.

Wannan mataki nasa ya jefa tsoro da rashin jin daÉ—i cikin mabiyansa, inda ake ganin hakan alama ce ta karuwar rashin amincewa a cikin tawagar tasa.

Aleru, wanda Gwamnatin Tarayya ta ayyana shi a matsayin ’dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, ya dade yana da hannu a sace-sacen mutane, kisan kai da satar shanu a Zamfara, Katsina da wasu sassan Sokoto.

Duk da wannan mummunan tarihi, yana cikin tattaunawar sulhu da kwamitin gwamnatin tarayya yanzu domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke addabar Arewa maso Yamma. Karanta rahoton Zagazola Makama a karkashin comment section.

Address

Mubi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mubi World News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mubi World News:

Share