
12/03/2025
Idan bakasan abu ba, yin shiru yafi alheri akan kayiwa mabiyanka bayani bisa rashin sani, karya, ko kuma son zuciya."
Mu Danyi wani karatu mana Amman muba analysis bane da zahiri muke amfani
Akwai wasu muhimman abubuwa da yawanci duk wani kutse da aka yi wa non-custodial wallet ta nan ake bi:
1. Key Logger Malware
Duk wanda ya dan samu wani basic a cyber security ya san yadda keylogger malware take da hatsari. A lokaci guda, zata iya capturing duk wani activity dinka, har da wallet address da seed phrases.
2. Phishing Attack
Wannan hanya ce mafi sauki kuma mafi rainin hankali da ake amfani da ita wajen sace wa mutane dukiya.
Za a kirkiri website ko wani app na karya wanda yayi k**a da na gaskiya.
Za a bukaci ka saka seed phrase, password ko wani login detail.
Idan ka saka, shikenan, hacker din yana ganin me kakeyi.
Duk wanda ya san wani abu akan phishing scam zai san yadda ake amfani da Termux wajen kirkirar clone website na Facebook, Twitter, da wasu platforms don karbar user data.
A kan wannan karatu, nayi me zaman kansa tun 2014, shiyasa ba wani kalar phishing da ban iya ba—tun muna amfani da waya har muka koyi aiki da Python.
Majority wanda aka sacewa Pi Network sun samu matsala ne ta phishing website dinnan da suke cewa ayi claim na 314Pi.
3. Remote Access Trojan (RATs)
Wannan mummunar virus ce wadda zata iya juyar da wayarka, in kira wanda nayi niyya, in yi transfer na komai da komai ba tare da na amshi wayarka ba—idan har na samu damar harba wannan virus din a kwakwalwar wayarka.
Ana amfani da download button na wasu websites da ke bada free downloads wajen saka wannan virus din. Idan wayarka ba ta da babban antivirus, zaka ga abubuwa 3 ko 4 suna downloading, kuma zasu yi force installing. Daga nan shikenan, kwanan ka ya kare.
4. Clipboard Hijackers
Akwai wata clipper wadda idan aka harba maka ita a waya ko computer, to duk wallet address da kayi copy zai canza maka da wani daban.
Irin wannan ya faru da mutane da yawa, s**a yi asara a asset dinsu.
KAR KA DORA LAIFI A KAN PI CORE TEAM
Baka da wata hujja da zaka ce Pi Core Team ne suke sace wa mutane dukiya.
Bayan Pi Core Team suna da 20 billion Pi Network a ajiye nasu ne na kansu.
Jama’a, idan ana fada muku magana, ku rinka dubawa sosai. Wallahi ana yaudarar mutane da yawa a space dinnan da sunan ilimi.