12/10/2025
Email yana daga cikin muhimman software da muke amfani da su a rayuwar mu tun daga wurin kasuwanci, karatu, aiki, ko harkokin sadarwa, amma kuma yana cikin hanyoyin da hackers ke yawan kai hari domin samun bayanan mu, wannan dalilin yasa yana da muhimmanci mu san yadda za mu kare Email ɗinmu daga masu kutse.
Na farko, idan kana da Email ko yanzu ka bude Email to ka tabbatar kana amfani da strong password, ma'ana kada ka rubuta Password dinka a matsayin sunanka, shekarunka, ko lambar waya, ka haɗa haruffa babba da ƙanana, lambobi da symbols irin wadannan (*, @, #*).
Misali, maimakon “Mustapha123”, zaka iya rubuta “Mu$t@ph@_2024”.
Na biyu, ka kunna two-factor authentication (2FA). shi ne zai zama kariya ta biyu da ake buƙata kafin a buɗe Email ɗinka.
Misali, idan wani ya samu password dinka kuma har ya samu damar shiga account dinka da password ɗin, to account din bazai bude gabadaya ba sai tsarin 2FA ya tambaye shi ya saka code ɗin da aka turo maka ta waya, kaga hakan zai hana shi samun damar shiga.
Na uku, kar ka taɓa danna link da ba ka yarda da shi ba. Akwai emails da suke zuwa k**ar daga “Bank”, “NCC”, “NITDA” ko “Google”, amma da gaske hackers ne ke aiko su domin su ja hankalinka ka danna link ɗin, dan haka idan baka da tabbaci, kada ka buɗe.
Na hudu, ka tabbata kana amfani da official app ko browser mai aminci, k**ar Chrome, Edge, ko Safari da ke da updated version.
Kada ka kasance mai yawan son shiga Email ɗinka ta hanyar free Wi-Fi ko system ɗin da mutane da yawa ke amfani da shi.
Na biyar, ka dinga canza password ɗinka lokaci zuwa lokaci a ƙalla sau biyu a shekara, hakan yana rage haɗarin samun sanin password ɗinka.
Idan kuma har wani ya samu damar hacking Email ɗinka, to ga matakan da zaka bi:
1. Ka shiga shafin account recovery na Gmail, Yahoo, ko Outlook (gwargwadon irin Email ɗinka).
Gasu link din shafukan k**ar haka:
1. Gmail: 👇
https://accounts.google.com/signin/recovery
2. Outlook 👇
https://account.live.com/acsr
3. Yahoo 👇
https://login.yahoo.com/forgot
Ka danna “Forgot Password” ko “Recover Account”. Daganan sai ka saka alternate Email ko recovery phone number, za su turo maka cod, da zarar ka dawo da account ɗin, ka canza password ɗinka nan take, kuma ka kunna 2FA domin kada hakan ya sake faruwa.
Sannan zaka iya tura report ga Kamfanin Email dinka akan wannan hacking din da ya faru dakai domin su warware matsalar ga link na support dinsu👇
Gmail: https://support.google.com/accounts/troubleshooter/2402620
Outlook: https://support.microsoft.com/account-recovery
A wannan zamanin hacker baya buƙatar sai ya sace maka waya domin ya samu bayananka, yana samun iko da Email dinka shikenan kuma shima din sai dai idan kai ne ka buɗe masa ƙofa, ka zama mai lura da tsaro a duk abin da kake yi online.
Email tamkar wayar mu ne gabadaya, idan aka samu iko dashi za'a iya goge komai na wayar mu, kuma za'a iya samun access da muhimman apps dake a wayar mu, musamman Apps na banki da sauran financial apps.
Allah yasa mu dace.