26/04/2026
Mahatma Gandhi, shahararren jagoran juyin juya halin wanda ya kwato wa ƙasar Indiya 'yancin kai kuma ya rayu tsakanin shekarar 1869 zuwa 1948, ya yi l tsokaci game da tarihin shugaban halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.
Lokacin da yake bayani game da yaɗuwar Musulunci, ya yi bayani a cikin jaridar Young India cewa: "Na ƙara tabbatarwa a raina cewa ba takobi ba ne ya samarwa da Musulunci mazauni zukatan mutane ba a wancan lokacin... A'a, zallar sauƙin kai ne, rashin girman kai na Annabin, cika alƙawarinsa, da kuma tsananin biyayyar da sahabbansa su ke yi masa da mabiyansa, da kuma jarumta da cikakken yakini ga Ubangijinsa. Waɗannan dabi'un su ne suke kakkaɓe musu dukkan matsaloli, ba takobi ba."
Gandhi ya ƙara da cewa, lokacin da ya gama karanta littafin tarihin Annabi (S.A.W) kashi na biyu, ya ji matuƙar baƙin ciki da aka ce littafin ya kare, saboda yana so ya ci gaba da karanta kyakkyawan tarihin wannan bawan Allah.
Idan har babban jagora wanda ya shahara da son zaman lafiya irin Gandhi zai ga waɗannan kyawawan halaye na gaskiya, riƙon amana, da sauƙin kai a matsayin sirrin cin nasarar Annabi (S.A.W), shin yaya ya kamata mu mu kasance a yau? Wane irin tasiri rayuwar manzon Allah ta ke yi a rayuwar mu da kuma mu'amala da waɗanda muke mu'amala da su a matsayinmu na mabiyansa?