09/02/2024
🌹DAUSAYIN YAN GWAGWARMAYA🌹
✍️ Aminu Muhammad Abdullahi
Dasunan Allah mai rahma Mai jinqai , tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi (s) da iyalansa tsarkaka .
Bayan haka Ina so indanyi wani kajeren rubutu dangane da mu'amalan da ke tsakanin samarin mu brothers and sisters (Soyayya) domin jiya naga wata Yar uwa a social media tayi qoqarin Amaye abinda yake cikin zukatan Yan uwa sisters akan sha'anin neman Aure (soyayya) inda take bayyana qorafin da yawancin sisters sukeyi cewa "kamar su brothers din Mafi yawan su basu iya soyayya din ba" sunfi ganin zunzurutun soyayya daga Amawa ta fuskacin (tallafawa,damuwa da damuwarsu, yin kyauta d.s) kamr yanda ta bayyana Alhamdulillh wnn Yar uwa ta yi qoqari sosai . Suma Kuma bangaren Brothers din ma zakaji suna yawan qorafi akan sisters sufi mata Amawa matsala ta fuskacin (Jin Kai ,Jan Aji,Girman kai d.s)
To ni a fahimta na Idan muka yi nazari akan soyayyar da Addini yazo da ita zakaga sun sha banban da soyayyar da gama Garin mutane keyi a yanxu , Shi mutum ma'aboci addini idan ya hadu da Dan uwansa ma'aboci addini zakaga Mafi yawan mu'amalar ta Addinin ce zasuyi hatta zantukkan a tsakanin su zakaga suna qoqarin ginasu ne 70% akan shari'a ne To Wann abin ne yake faruwa a soyayya Yan uwa brothers and sisters kenan , ko wannensu yana iya qoqarin ganin Bai tsallaka iyakar shari'a ba kar Dan uwansa y ganshi wani iri sabanin idan da dayan yakasance ba'ame zakaga Gamagarin soyayya zaizo dashi wacce ita Kuma tafi impressing Masoyi domin har iyakar Yana iya tsallakawa domin burge ta /shi , sbd already soyayya ta hadasu ba Addinin ba don haka ba zai yiyu Alaqar yazama kala daya ba. Lallai zaka/zaki iya samun cikakkiyar abinda soyayyar zamani ke buqata to Amma tabbas akwai Hatsari domin DUK abinda aka sabawa shari'a a cikinsa dole sai anga sakamako marar kyau da kan iya Kai Dan uwa ko Yar uwa samu (wrong partner). Wanda kuma wnn yafi CUTAR Da Yan uwa sisters domin kuwa hatta ruhin gwagwarmayar ta Yana iya samun matsala musamman in tana matuqar son sa komai na iya faruwa da sister da ta aure Ba'ame kanama iya nemanta a Harkar ka rasa wa'iyazu billah.
JARABAWA : Kuna tunanin mu zamo maabota Addinin Kuma Allah yaqi jarrabamu ??? Kutuna pa mu samari ne Maza da mata Wanda kusan duk motsin mu wunqunri da hanqoro muke na ganin Addinin Allah y tabbata to kunga lazeem ne Allah ya jarrabamu ta ko wanne janibin rayuwar mu, to mufahimchi Wann abun jarrabamu akeyi DUK wann kyale-kyalen soyayyar da muke ganin munrasa a tsakani Duk jarrabawa ne idan muka qoqarin jurewa Wann yanayin to munchi jarrabawar Kuma tun nan Duniya zamuga Natijar Hakan kafin muje Gobe daga karshe zakaga Ahlul-wilaya ne ke auren Ahlul-wilaya .
Daga karshe zan bamu shawara Baki dayan mu
Brother : Mukasance masu sauraren qorafin inda muka kubsa a zamantakewar mu sisters domin yin kyara matuqar Bai sabawa shari'a ba , Mukasance masu Neman ilmi, Aikin yi, Yan gayu, masu yawan hidimtawa karkazamo kanqamo zuciya ta na son Mai kyautata mata, mukula da wnn time din fira akan Gwagwarmaya daban time din da zaka ware ka zazzaga mata kalaman soyayya daban mlm. Karka ce kullum wa'azi ne tadin 🙈 D.s
Sisters: ku kasance masu aiki da kwakwaken akan korafin da brothers suke yawan yi domin kyara da kaucewa fadawa Hannun Ba'ame, a same ku da tausayawa, hidimtawa,kauda Kai daga abin duniya, sauke jin Kai,Haquri ,nutsuwa,rage buri, da godiya da abinda aka samu D.s .
Insha Allah ta wannan hanyoyin za'a rage samun matsaloli tsakanin samarin brothers and sisters 🥰 Da fatan Allah y tabbatar da mu akan Hanyarsa duk rintsi🤲