16/01/2026
Manzon Allah {ﷺ} ya ce: Mafi tsananin jarrabawa a cikin mutane su ne Annabawa, sai waɗanda s**a fi kamarsu (imani da kyawawan ayyuka), sannan waɗanda ke biye da su.
Ana jarrabar mutum gwargwadon addininsa; idan addininsa yana da ƙarfi, sai a ƙara masa jarrabawa. Idan kuma addininsa yana da rauni, sai a rage masa. Kuma jarrabawa ba ta gushewa daga bawan Allah har sai ya riƙa tafiya a cikin mutane alhali babu wani zunubi a kansa.
[ƘARIN HASKE]
Dalilin da ya sa Annabawa s**a fi shan Wato jarrabawa: Saboda matsayinsu mafi girma a wajen Allah, da cikakken imani da hakurinsu. Jarabawa tana ƙara ɗaukaka darajarsu. Sannan
Jarabawa tana gwargwadon imani Mutum mai ƙarfi a addini yana iya ɗaukar jarabawa mai tsanani, shi ya sa Allah ke ƙara masa domin ƙara lada da tsarkake shi.
Rahama ga mai raunin imani: Idan kuwa imanin mutum bai da ƙarfi, Allah yana rage masa nasa jarabawa domin kada ta karya shi, To wannan rahama ce daga Allah.
Jarabawa na kankare zunubai: Cutarwa, talauci, damuwa, ko wata wahala da Musulmi ya kan ai fuskanta da hakuri, suna zama kaffarar wannan zunubansa har ya zama tsarkakke.
Darussan da ake koya daga Hadithsin: Kada Musulmi ya yi zaton jarabawa alama ce ta ƙin Allah, Jarabawa na iya zama alamar ƙauna da ɗaukaka daga Allah, da Hakuri a kan jarabawa hanya ce ta samun gafara da lada mai yawa, da
Dole Musulmi ya ƙarfafa imaninsa, domin kuwa jarabawa wani ɓangare ne na rayuwa.
_Duk wanda yayi nuni akan aikin alkhairi kamar ya aikata ne._
*Allah yabamu iko ameen 🤲🏼