01/01/2026
TARIHI
A RANA IRIN TA YAU: 12 Ga Watan Rajab
1.
وفاة عمّ النبي (ص) العباس بن عبد المطلب بن هاشم بن عبد مناف سنة 32هـ، ودُفن في البقيع إلى جنب الأئمة الأربعة (ع).
A irin wannan rana ne Kawun Manzon Allah (S.A.A.W), Sayyid Abbas bn Abdul-Muɗɗalib (A.S) ya rasu a shekara ta 32 bayan Hijira. Wannan na nufin ya rasu kimanin shekara 22 ko 23 bayan wafatin Annabi (S.A.A.W). An binne shi a Baƙi’a, ƙabarinsa yana kusa da ƙanurburan A’immatul Baqi’a (A.S).
2.
دخول أمير المؤمنين (ع) إلى الكوفة واتخاذها مقرّاً لخلافته، وذلك بعد حرب الجمل سنة 36هـ.
Har wayau a irin wannan rana a shekara ta 36 bayan Hijira, Imam Amirul-Mu’minina Ali (A.S) ya shiga Kufa, inda ya mayar da ita hedkwatar (cibiyar) halifancinsa. Wannan ya faru ne bayan Yaƙin Jamal, wanda aka yi da Ummul-Mu’minina A’isha da magoya bayanta.
3.
هلاك معاوية بن أبي سفيان في دمشق سنة 60هـ، ودُفن في الباب الصغير، وقد أورد ابن خلكان في ترجمة النسائي أنّه لما سُئل عن فضائل معاوية قال: ما أعرف له فضيلةً إلا قول النبي (ص): «لا أشبع الله بطنك».
A irin wannan rana ne a shekara ta 60 bayan Hijira, Mu’awiya bn Abi Sufyan, sarkin Sham mai tawaye, ya mutu a Damashƙa inda aka binne shi a wurin da ake kira Babus-Saghir (wanda a yau aka ce ya zama wurin zubar da shara).
Ibn Khalikan ya ruwaito a cikin tarjamar Nisa’i cewa, lokacin da aka tambaye shi game da falalar Mu’awiya, sai ya ce:
“Ban san wata falala da yake da ita ba, face addu’ar da Annabi (S.A.A.W) ya yi masa.”
Addu’ar ita ce:
لا أشبع الله بطنك
“Kada Allah ya ƙosar da shi.”
Dalilin wannan addu'ar kuwa shi ne: Wata rana Annabi (S.A.A.W) ya aika a kira Mu’awiya sai aka ce masa yana cin abinci,
Annabi ya sake aikawa kiransa a karo na biyu, har sau uku, amma Mu’awiya ya jinkirta saboda cin abinci sai Annabi (S.A.A.W) ya ce: Allah kada ya ƙosar da cikinsa. Wannan na nan a ruwayoyi daban-daban na Sunnah, musamman a Sahih na Muslim.
اللهم صلِّ على محمدٍ وآلِ محمد