20/05/2026
Atiku ya yi alkawarin magance matsalar tsaro da farfado da tattalin arzikin Nijeriya idan aka zabe shi
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito mai taimaka wa Atiku Abubakar kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya ce zaman tantancewar ya wuce tsarin jam’iyya kawai, yana mai bayyana cewa Atiku ya gabatar da muhimman tsare-tsare kan tsaro da tattalin arziki ga kwamatin jam'iyyar ADC.