18/07/2023
Mu Rayu Cikin Salama!
Mu Ba Ma'asumai Bane Muna Saɓawa Ubangiji Amma Muna Neman Gafarar Sa Dan Shine Ya Chanchanta.
Dan Adam Ajizine Mai Laifi Ko Kuskure Ga Mahalicci Ko Ga Wani Abokin Halittar Mu.
Muyi Rayuwa Cikin Girmama Manya, Sa'annin Mu Har Ma Da Wanda Muka Fisu. Dan Bani Da Buƙata Ga Wani Hakan Kada Yasa Mu Zamo Masu Nuna Isa, Rashin Girmamawa Ko Rashin Mutuntawa. Matsayin Kai Ƙarami Ne Akwai Abu Koda An Maka Wanda Ya Taɓa Zuciyar Ka Kayi Kokarin Zama Kaine Da Mallakin Zuciyar Ka Ba Itace Zata Mulkeka Ba. Wanda Dayawa Daga Matasa Masu Tasowa Kamar Mu Suke Gaza Fahimta Kenan Duk Da Koni Ban Fi Karfin Hakan Ba Sbd Ajizanci Da Rauni. Domin Mu Nuna Ladabin Mu Sai Mu Haƙurtar Da Zuciyar Mu A Dole Badan Ta So Ba, ( Mu shagalta Da Abinda Ke Faranta Ran Mu; Karatun Qur'ani, Karance Littafai, Duba Labarai, Jin Waƙa Yin Bacci DSS) Ina Mai Tabbatar Idan Mukayi Daya Daga Abinda Ke Sanya Nustuwa Idan Muna Damuwa Zamuji Hamdala Da Kin Daukar Mataki A Lokacin.
Mu Tsaftace Alakar Mu Da Kowa.
Matsayin Ka A Babba Kafi Na Ƙasa Dakai Shekaru, Sanin Duniya Har Ma Ilmi Ana Kyautata Zato Babba Na Sama Akan Karami. Ya Kyautu Kuja Na Ƙasa Daku Jiki Ku Nuna Musu Abu Kaza Mai Kyau Ne, Ku Ƙara Himma Akai. Abu Kaza Baya Da Kyau B***e Amfani Sannan Baya Kai Mutum Ga Nasara. Cikin Salo, Hikima Da Fasaha Na Ƙasa Daku Zasu Zamo Mallakin Ku Ba Tare Da Ɗaga Kai Da Nuna Fifiko Ba.
Daga Manya Za'a Gane Na ƙasa Yadda Zasu Kasance.
Shi Yaro Akwai Wauta, Kuruciya Da Ganin Shima Girma Ya Kawo Masa Dan Haka Bazai Juri Wasu Ababeba Da Za'a Masa Ba, Dole Sai An Jawosa Jiki Za'a Fahimtar Dashi Rayuwa.
Duk Abinda Muke Bukata Bai Wuce Zaman Lafiya!
Ina Mai Fata Da Rokon Allah Yasa Wannan Rubutu Yayi Tasiri Ga Na Ƙasa Damu, Mu Da Kuma Manyan Mu. Ameen.
Idan Akwai Wani Kuskure Na Ko Laifi Dan Allah Ku Fadamin. Nagode Allah Yabar Zumunci Tsakanin Mu Da Ku.
Mubarak Abubakar ✍️
Mubarak Alhaji Garba
17/07/2023.