19/04/2025
Yarima Al-Waleed bin Khaled bin Talal, wanda aka fi sani da “Yariman Barci” a fadin duniya ta Larabawa, ya cika shekaru 36 a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu, duk da cewa yana cikin dogon suma da ya kwashe fiye da shekaru 20 a ciki.
Ya samu suma ne a shekarar 2005 bayan mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a birnin London.
A cikin sa’o’i 24 da s**a gabata, ranar zagayowar haihuwarsa ta janyo hankalin mutane da dama a kafar X (Twitter), inda dubban masu amfani da kafar s**a wallafa addu’o’i, fatan alheri da tunatarwa game da wannan lamari da ya zama wata alama ta bangaskiya da jimiri.
Duk da tsawon lokacin da ya dauka a cikin wannan hali, yariman na ci gaba da samun kulawa ta musamman, yana dogara da na’urorin taimaka masa numfashi da abinci ta bututu. A shekara ta 2019, an bayyana cewa ya nuna wasu karancin motsi kamar daga yatsa ko motsa kai kadan, amma ba su nuna cewar ya farfado gaba ɗaya ba.
Yanzu haka yana karɓar kulawa a Cibiyar Lafiya ta Sarki Abdulaziz da ke Riyadh, karkashin kulawar kwararrun likitoci.
Iyayensa, ciki har da mahaifinsa Yarima Khaled bin Talal da mahaifiyarsa Gimbiya Reema bint Talal, na ci gaba da nuna cikakken fata da bege. A baya, Gimbiya Reema ta bayyana cewa “ransa har yanzu yana nan a jikinsa,” yayin da Yarima Khaled—wanda ya ki cire na’urorin taimako—ke ci gaba da tsayawa da yakinin cewa “Wanda Ya raya ransa tsawon wadannan shekaru, Shi ne Zai iya warkar da shi.”
Babu wani sabon bayani na kiwon lafiya da iyalansa s**a fitar dangane da wannan zagayowar haihuwarsa. Sai dai irin yawan goyon bayan da ya samu a kafafen sada zumunta na nuna yadda labarinsa ya ci gaba da zama abin tausayi da haɗin kai ga mutane a sassan yankin.
Masana sun akwai yiwuwar ya farfado bayan dogon lokaci irin wannan abu ne da ba kasafai yake faruwa ba, sai dai suna ci gaba da fatan sabbin ci gaba a ilimin kwakwalwa da jijiyoyi na iya kawo mafita nan gaba. A yanzu dai, ba a sami canji a lafiyarsa ba.
ATP News ✍️