
15/09/2023
FIRST AID GROUP OF FITYANUL ISLAM OF NIGERIA, SOUTH-SOUTH NATIONAL ZONAL HEADQUARTERS.
Sakon Murnan Zagayowar Watar Haifuwa Fiyeyyen Hallitta Annabi Muhammad (SAW):
Amadadin manya Shu'abanin da Membobin kungiyar Agajin fityanul Islam na kudu-maso-kudancin kasa wato (South-South) da kasa Baki daya.
Kungiyar Agajin Fityanul Islam tana Taya ilahirin Al'umma musulmai Masoyan Allah, Masoyan Manzo Allah (Sallallahu Alaihi Wassallam 💞) MURNA Zagayowar Watar Haifuwa Fiyeyyen Hallitta Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wassallam 💞).
Shu'abanin kungiyar sunyi Kira tare da gargadi da Jan hankalin Membobi da Yan Agajin Fityanul Islam na kasa Baki daya, da su jajirce wurin kullawa da hakkin al'umma tare da bada tsaro a wuraren mauludin bana. Sun Kara da cewa duk wani musulmi yayi/tayi koyi da kyakkyawar dabi'un MA'AIKI(SAW) da addu'o'i zaman lafiya da mawiyacin Hali da kasa take Ciki.
Ubangiji Allah ya sada mu da dukkan alkhair dake cikin wannan wata, Allah ya kawo mana sauki sadan rayuwa da ake Ciki da zaman lafiya a kasar mu Baki daya da duk inda al'umma musulmai suke alfarman shugaban rahma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wassallam 💝
✍️HARUNA HASHIMU YILMUT,
Zonal Information, South-South.
16/9/2023, 1/Rabi'ul Awwal/1445AH.