25/07/2021
🎤MUYAR AL'UMMA🎤
GARGADI NAMUSAMMAN AGAREKU MATASAN JAHAR YOBE
Matasa kune ginshikin al'umma, bacinku daliline na daidaicewar al'umma dakuma maida jaha, yanki, kokuma kasa tazamo cibaya acikin sauran kasashe nakusa dana nesa. Dawannane wasu daga cikin bata garin yansiyasa, shuwagabbani kokuma masu fada'aji ke amfani da kuruciyarmu domin kyautata gobensu dana y'any'ansu tahanyar cusamana kabilanci, bangaranci, bangar siyasa koku maroka bayan sunbarmu da yunwa, talauci, da rashin aikinyi.
karkumanta suwannan, y'ansiyasar, sarakunan kokuma masu fada'aji da kuketa kunfar baki harkuketa fada dajunanku akansu, basuma san kunayiba, asalima bakuda wani daraja agunsu, yauda wani abu zaisameku babu daya acikinsu dazai bada rayuwarsa kokuma jinininsa dominku. Kar kumantafa dasaninsu takawa keshan wahala abangare narayuwa dadama, musamman idan mukayi la'akarida yadda al'amarin tsaro yalalace idan kakai kara saikabiya, Belly saikabiya, idan anturaku koto saika biya, indan kadebi ma'akaita kuka kamo masu laifi saikabiya kudin manmota, abun baitsaya ananba yanzufa Talaka bai'isa yayishari'a da maikudiba sabida koyayi bazaici nasaraba koda kuwa shine da gaskiya sabida lalacewar wasu dagacikin jama'an tsaro, hartakai al'umma sun kwammabace subari da Allah.
Abangare likitoci kuma abun ba'a magana, walakancin da al'umma kefuskanta ah asibitocin gomnati, hartakai likita yakifitowa aiki sai karfe goma kokuma tara nasafe alhalin majinyata najiranshi, zuwa karfe shabiyu kuma sutashi alhalin ga majinyata kacakaca abun baitsaya ananba hartakai al'umma suna tsoron likitoci ah asibitoci gimnati tamkar dodonni sabida zabar walakancinsu bayan hakan yasabawa kundin tsarin mulki nakasa damu daku duk munsani kuma suway'annan yan siyasan, sarakuna kokuma masufada aji dakuketa kunfar baki akansu sunaji kuma sunagani amma babu wanda yataba fitowa yace kala sabida su kasashenwaje sukekai y'ay'ansu.
Dawannane muke gargadin al'umma tare da janhankalinku akan abunda yashafi cigaba al'umma jaha dakuma kasa bakidaya, hadinkanku nada mahimmanci.
📝📝Sing
Potiskum Broadcasting Corporation