01/06/2022
Assalamu Alaikum warahmatullah!
A dai-dai lokacinda al'umma, musamman ta ƙasar nan take ta tunanin waye zata zaɓa domin share mata hawayenta daga koke-koke marasa ƙarshe da gwamnatin da ma waɗanda s**ayi mulkin k**a karya kafinshi, kuma al'ummar ta kasance tana ta leƙe-leƙe domin gano wani mai kyau, duk inda ta leƙa babu cikakkiyar mafita, ta rasa yanda zatayi, tana neman dama-dama ido rufe, muke masu bata shawara mai buƙatan ta lura dashi da kyau.
Acikin wannan yanayi matsanaici da muke ciki, yanayi na la haula, yanayinda gwamnatin da ke gudanarda al'umma batada hukunci kan wanda ya aikata , sai dai **e. Bata hukunta ƁARAWO da hukuncinda Allah (T) ya umurci Al'ummar da ya halitta su hukuntashi dashi, Batada hukunci kan wanda ko waɗanda s**ayi , dukda ya faɗa a cikin littafinshi mai tsarki cewa: "Wanda ya kashe mutum ba tareda haƙƙi ba, k**ar ya kashe mutanen dake doron ƙasa baki ɗayansu ne", lokacinda aka ajiye umurnin Allah (T) a gefe, musulmai suna gani da idanuwansu, suna numfasawa da lafiyansu, suna rayuwa da hannayensu da ƙarfinsu, kuma suke tunanin sauƙi daga wurin Allahnda s**a ƙi ɗaukaka kalmarshi, ina hakan zai yiwu fisabilillah?
Muyi dogon nazar mana!
A dai-dai wannan gaɓa ne muke nuni ga al'ummarnan cewa akwai mafita daga cikin wannan ƙangi. Mafitar kuwa itace kalmarnan da ba'a son ji. Itace komawa ga cikakkiyar ma'anar "LA'ILAH ILLALLAH"
Wani na iya cewa; toh ai yanzuma "LA ILAH ILLALLAH" kam da ita mukayi riƙo. Sai mu ce maka kana taƙaita ma'anarta ne a wuri guda. Duba bayanai guda uku masu zuwa k**ar haka:
1. A lokacin manzonmu (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalan gidanshi tsarkaka, da sahabbanshi managarta), azzalumai da yayi yaƙi da zaluncinsu suna fakewa da bautar gumaka ne suna ƙwace ma mutane suna kuma bada umurnin san ransu da sunan waɗannan iyayen giji. Manzonmu mai rahama yayi yaƙi da su da "Babu abin bauta koma bayan Allah makaɗaici". Ya kuma ci nasara!
2. Lokacinda Shehu Usman Ɗanfodiyo ya zo ya jaddada addini a wannan nahiya, sarakunan gargajiya ne suke mulkin k**a karya ma al'umma. K**a daga ciyawar da dabbobinku suke ci, ruwan shansu, bishiyoyinku, filaye, harma muhallinku duka na sarki ne. Shi yasa ma wajibi ne kan kowa ya biya JANGALI (haraji) na amfani da dukkanin abubuwanda sarki ya mallaka. Shehu yayi yaƙi da azzaluman sarakuna tare da aiki da wannan kalma "BABU SARKI SAI ALLAH". Kuma ubangiji, masoyin aikinda shehu ya aikata ya bashi nasarar ƴanto al'umma daga ƙangi bayan gwagwarmaya da al'ummar s**a bada haɗin kai akayi da goyon bayansu. Ma'ana tare dasu.
3. Imam Ayatullah, Sayyid Al-musawi Khomeini da ya samar da jamhuriyar musulumci ta Iran, ya ci nasarar kafa gwamnatin musulunci a lokacinda ƙasar take ƙarƙashin mulkin k**a karya na Shah. Wanda Imam yaci nasarar hakanne ta hanyar goyon bayanda ya samu ta hanyar faɗakarda mutane kan komawa ga addininda Allah ya ɗorasu a kai. Yin biyayya ga wannan gwamnatin dama irinta dai-dai yake da kaucewa daga kan tsarinda Allah ya ɗorasu a kai ne. Komawa gareshi kuma komawa ƙarƙashin rahamar Allah ne. Ya yi amfani da "BABU GWAMNATI SAI TA ALLAH" ya kuma sami cikakkiyar taimako daga mai amfani dashi wurin aikata wannan gagarumin aiki wato Allah (T).
Toh, in zamu lura, mu cire tsoron wanin Allah, zamu ga cewa haƙiƙa a wannan ƙasa tamu, kuma a wannan zamanin, akwai bawan Allah da aka tasar mana domin yi mana jagora wurin ƙwato kawukanmu daga hannun waɗanda basa kusa da Allah ko kaɗan. Wanda haƙiƙa, ba makawa zai aikata irin aikinda Imam Khomeini ya aikata a Jamhuriyar musulumci ta Iran a lokacinda ake kallon hakan BAZAI YIWU BA. Kuma ake mishi kallon mai yaƙi da gwamnati mai cikar iko. Ya rage namu mu mara mishi baya al'amarin ya yiwu cikin ƙanƙanin lokaci, Ko kuma mu cigaba da bin san zuƙatanmu da tsoron mutuwa (wanda tana iya zuwa maka a lokacinda kake tafiya, zaune, kan abin hawa, harma lokacinda kake aikata saɓo, bare mutuwa kan hanyar Allah wanda matsayinta shahada ce) da bin malamai masu son zuƙatansu kuma Allah yayi amfani da wasu ba mu ba. Amma dai alƙawarine zai cika haskensa.
Allah ya shige mana gaba!
©
Reawakening Pens is a non business page purposely for awareness and enlightenment about everything regarding "Harka Islamiyya".
It shares informstioms that are also relevant. Help in promoting it by inviting everybody to here.