25/11/2025
NDYC Ta Caccaki Wike da INEC Kan Yunkurin Rusa Dimokuraɗiyyar Najeriya
Ƙungiyar Niger Delta Youth Congress (NDYC) ta yi taron ’yan jarida domin bayyana damuwa kan yadda Ministan FCT, Nyesom Wike, da kuma yadda INEC ke nuna rashin adalaci game da sakamakon gangamin PDP na Ibadan ke zama babbar barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
NDYC ta zargi Wike da amfani da muƙaminsa wajen tsoma baki cikin jam’iyya, tayar da rikici, tsoratarwa da kokarin tilasta ra’ayinsa, abin da ke yi wa tsarin dimokuraɗiyya mummunar illa. Ta ce halayensa na nuna girman kai, raina doka da neman iko su na iya tarwatsa ƙasa.
Kungiyar ta roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi Wike, ya tunasar da shi cewa shi bawa ne na jama’a, ba sarki ba.
A bangaren INEC kuwa, NDYC ta nuna damuwa kan yadda take jan kafa wajen tabbatar da zababben shugaban PDP Kabiru Turaki, tana nuna fifiko ga Damagum. Ta ce wannan ya tauye adalci, ya kuma lalata amincewar jama’a da hukumar zabe.
NDYC ta jaddada cewa sakamakon taron Ibadan halastacce ne, kuma INEC dole ta tsaya kan doka ba tare da shiga hannun masu son murde sakamakon siyasa ba don biyan buƙatar Wike.
Ta kuma bayyana cewa halayen Wike ba sa wakiltar mutanen Niger Delta gaba ɗaya.
A ƙarshe, NDYC ta ce za ta ci gaba da kare dimokuraɗiyya da doka, domin Najeriya ta fi kowane mutum girma, kuma duk wanda ya yi barazana ga tsarin mulki dole a tsawatar masa.
Da hannun
Comr. Israel Uwejeyan, National Coordinator, NDYC