
19/06/2025
JARIDUN WASANNI.
Barcelona ta cim ma yarjejeniya ta baki tare da ɗanwasan gaba na Athletic Bilbao Nico Williams, amma har yanzu akwai sauran aiki kafin ya zama ɗanwasanta.
Ɗan ƙasar Sifaniyan da ya ci wa Bilbao ƙwallo 31 a wasa 67, ya ja hankalin ƙungiyoyi kamar Arsenal da Bayern Munich a wannan bazarar.
Williams mai shekara 22 ya nuna amincewarsa da yarjejeniyar shekara shida, wadda za ta ba shi damar haɗewa da abokin wasansa a Sifaniya Lamine Yamal a filin wasa na Nou Camp.
A farkon makon nan ne shugaban sashen wasanni na Barca, Deco, ya gana da Williams a Ibiza, inda a nan ne s**a cim ma yarjejeniyar da baki.
Tun da farko Barcelona ta nemi ɗaukar Luis Diaz daga Liverpool amma sai farashinsa na fan miliyan 80 da aka nema ya sa ta ja da baya.
Sai dai farashin da ke cikin kwantaragin Williams bai wuce yuro miliyan 62 ba a Bilbao, wanda Barca take ganin za ta lalewa domin sayensa.
Duk da yunƙurin nata, Barca na cikin halin matsi sosai a fannin kashe kuɗi.
👏Rahotonni daga birnin Landan na cewa ɗanwasan tsakiyar Arsenal da Ghana, Thomas Partey, na shirin barin ƙungiyar yayin da s**a kasa cim ma matsaya a tattaunawarsa da kulob ɗin game da sabon kwantaragi.
Kafar yaɗa labarai ta ESPN ta ce majiyoyi sun shaida mata cewa ba a tsammanin ɗanwasan mai shekara 32 zai sake ƙulla yarjejeniya da kulob ɗin na arewacin Landan.
A ƙarshen watan nan na Yuni kwantaragin Partey zai ƙare, wanda ya koma Arsenal daga Atletico Madrid kan fan miliyan 45 shekara biyar da s**a gabata.
Tsohuwar Atletco da Barcelona da kuma wasu daga Turkiyya sun nuna sha'awar ɗaukar ɗanwasan.
👍Yayin da aka kammala wasannin farko a zagayen cikin rukuni na gasar kofin duniya ta Club World Cup, rawar da ƙungiyoyi daga nahiyar Afirka s**a taka ba ta yi kyau ba zuwa yanzu.
Memolodi Sundowns ta Afirka ta Kudu, da Al Ahly ta Masar, da Wydad Casablanca ta Moroko, da Esperance ta Tunisia ne ke wakiltar nahiyar a gasar da aka faɗaɗa zuwa tawagogi 32.
Al Ahly ce ta buɗe gasar da wasa tsakaninta da Inter Miami ta su Lionel Messi, inda s**a tashi 0-0. Ana iya cewa ba yabo ba fallasa a wasan nasu.
Sai kuma Esperance da ta sha kashi 2-0 a hannun Flamengo ta Brazil a Rukunin E ranar Talata, yayin da ita ma Wydad Casablanca ta sha kashin 2-0 a hannun Manchester City ta Ingila ranar Laraba.
Memolodi Sundowns ce kaɗai ta samu nasara 1-0 a kan Ulsan HD ta Koriya ta Kudu ranar Laraba a wasansu na Rukunin F.
Ko za mu ga sauyi nan gaba? Lokaci ne kawai zai bayyana hakan.
👏Sabon mai horarwa Xabi Alonso ya fara da canjaras a wasansa na farko da ya ja ragamar Real Madrid a karawar da s**a tashi 1-1 da Alhilal ta Saudiyya.
Shi ne wasan farko a zagayen rukuni da s**a fafata a birnin Miami na Amurka, inda Francisco Garcia ya fara ci wa Madrid ɗin ƙwallo tun a minti na 34.
Ana dab da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma Ruben Neves ya farke wa Al Hilal daga bugun finareti.
Madrid da Al Hilal na cikin Rukunin H tare da Salzburg ta Austria da Pachuca ta Mexico, yayin da Salzburg ta ɗare saman teburin bayan doke Pachuca 1-0 tun da farko.
DAUDA GARBA BIN-APPAN POTISKUM