
06/08/2025
Wata malama a cikin wata makaranta tana so ta karfafa gwiwar ɗalibanta, sai ta yanke shawarar shirya musu jarabawa. Wanda duk ya samu nasarar cin cikakken maki, zata bashi kyautar sabon takalmi.
Yaran sun yi farin ciki da wannan gasa, sai kowannensu ya fara rubutu da ƙwazo.
Amma abin mamaki shi ne bayan tattara takardun, dukkaninsu sun amsa da kyau kuma sun samu cikakken makin da ake bukata.
To wa za a ba kyautar?
Malamar ta godewa kowa bisa ƙoƙarinsu… amma sai ta shiga ruɗani kan wanda za ta ba kyautar domin kowa ya samu cikakken maki.
Sai ta tambaye su su ba da shawara mai kyau don a zaɓi wanda zai karɓi kyautar bisa yardar kowa.
Ra'ayin ɗaliban shi ne kowannensu zai rubuta sunansa a wata takarda sai ya nade, ya saka a cikin wani kwali, daga nan sai malamar tazo ta zaro ɗaya daga cikin takardun a gabansu. Duk wanda sunansa yake jiki shi ne ya lashe kyautar.
Haka aka yi. Malamar ta zaro takarda guda daga cikin kwalin a gabansu ta karanta suna: "Laure Bashir" — ita ce tayi nasara. Ta zo gaba don karɓar kyautarta.
Laure ta matso gaba cike da farin ciki ga hawaye na zubo wa daga idonta, yayin da malama da dukkan sauran yaran ke tafa mata.
Ta gode wa kowa sannan ta rungumi malamarta bisa wannan kyauta mai ban mamaki a gareta, wacce ta zo daidai lokacin da take buƙatar ta.
Domin ta gaji da sa tsohon takalminta wanda iyayenta ba su da ikon siya mata sabo saboda tsananin talaucinsu.
Malamar ta koma gida cikin farin ciki… Lokacin da mijinta ya tambaye ta game da labarin, sai ta gaya masa tana kuka.
Mijin ya ji daɗin labarin, amma ya yi mamakin dalilin kukan matarsa. Ya tambaye ta dalilinta, sai ta ce:
"Lokacin da na koma gida na buɗe sauran takardun, sai na gano cewa dukkan yara sun rubuta sunan ɗalibar nan ne – Laure Bashir – maimakon nasu.”
Yaaa Allah!!
Yaran sun lura da halin da Laure ke ciki, sai s**a haɗe kansu tamkar yan'uwan juna domin su sanya farin ciki a zuciyarta…