
01/09/2025
Rikicin ƴan bindiga ya sake ƙazanta a ƙaramar hukumar Shagari ta jihar Sakkwato, inda aka kashe aƙalla mutum biyar tare da yin garkuwa da limamai da hakimin garin Rinaye.
Shaidu daga yankin sun ce hare-haren sun ci gaba tsawon kwanaki uku a jere, inda ƴan bindigar ke kai farmaki ƙauyuka daban-daban, suna kashe mutane tare da sace wasu, ko a garin Rinaye, an tabbatar da cewa sun yi garkuwa da mai garin da limaman garin, bayan sun kashe mutum uku.
Rahotanni sun nuna cewa sama da ƙauyuka goma sun watse sak**akon tsanantar hare-haren, lamarin da ya tilastawa daruruwan mazauna yankin yin zanga-zanga a babbar hanyar da ta haɗa Sokoto, Kebbi da Neja domin nuna fushi da rashin kulawar gwamnati agare su.
Wasu daga cikin mutanen da abin ya shafa sun ce ba su da wani tallafi daga gwamnati ko jami’an tsaro, inda s**a yi kira da a kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Hukumomin bayar da agajin gaggawa na ƙasa dana jihar NEMA da SEMA sun tabbatar da samun rahoton ƴan gudun hijira daga yankin, inda s**a ce sun kai ziyara wasu rukunin gidaje da s**a karɓi waɗanda s**a tsere daga hare-haren.