03/07/2025
Babban Asibitin Rano: A Ina Matsalar Ta Ke?
Da farko dai ban so na ce komai ba, amma wannan saƙo ya ƙara min ƙwarin gwiwa na cewa wani abu a kan matsalolin babban asibitinmu na Rano.
Na samu Rahotanni kan yadda marasa kishi suke illata mana wannan asibiti ta hanyar sace kayayyakin aiki na miliyoyin nairori da gwamnatin Ganduje ta saka a bangarori dabam-dabam na asibiti tun bayan ɗaga likkafarsa zuwa babban mataki.
Kusan dukkanin kayan aikin da aka zuba a wannan asibiti na zamani a kan idona aka saka su, wasu kuma daga baya na kan kai ziyara domin gani da ido. Na san cewa an kashe maƙudan kuɗaɗe millions of naira wajen inganta mana wannan asibiti da waɗannan kayayyakin aiki, wadda ko Asibitin Murtala ma ba shi da irin wasu kayayyakin da aka zuba mana.
Amma fa a yanzu an mayar da mu baya, bayan-baya ma, domin an sace da yawa daga cikin waɗannan kayayyaki, kai hatta batiran Solar na samu rahoton cewa ana zuwa ana sace su ɗaya bayan ɗaya. Saboda rashin sanin kai sakacin namu ya kai hatta karafunan windows ɓallesu ake yi ta ƙarfin tsiya ana sacewa. Haba jama'a? Kuma a haka sunan muna da shugabanni kenan? Sunan muna da Dattijan yanki da a baya s**a dage cewa sai Jami'an lafiyarmu sun sadaukar da kai domin bawa yankin gudunmawa?
Ina shugaban ƙaramar hukuma, ina ɗan majalisar Jiha, ina ɗan majalisar tarayya? Ina Sanatan yankinmu? Ina girma da tasirin masarautarmu? Duk kishin yankin namu a baki yake kenan?
Shin girman wannan matsala bata kai a ce zuwa yanzu dukka masu faɗa a ji sun zo sun haɗa kai domin ɗaukar matakin gyara ba?
Ina zargin dole da ɗan gari a kan ci gari, domin ƙwarya-ƙwaryan bincike da na fara yi, ya tabbatar min da cewa wannan mummunar sata da ɓarna ta kayayyakin asibitinmu, da ma sakaci wajen gudanar da wasu ayyukan, akwai sa hannun wasu manyan asibitin da ba kishin yankin ne a gabansu ba. Muna roƙon kwamitin dattijai da cigaban yankinmu su gaggauta bincika lamarin nan tare da ɗaukar mataki domin hukunta duk waɗanda suke da hannu a cikin wannan lamari komai girmansu, kuma a ɗauki matakin kiyaye afkuwar hakan a gaba.
Wannan kira, matakin farko ne na ɗaga muryarmu game da wannan mummunan al'amari da ya shafi al'ummarmu. Allah Ya sa ya zama silar samun gyara.
Fatan Alheri ga kowa🙏🏼
©️ Ibrahim Ɗan'uwa Rano