22/08/2025
Za a shafe kwanaki 3 ana mamakon ruwan-sama a Najeriya - NiMet
Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da yiwuwar samun ruwan sama da iska daga ranar Juma’a zuwa Lahadi a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewar rahoton da ta fitar, jihohin Arewacin ƙasa k**ar Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Yobe da Taraba za su fuskanci guguwar iska da ruwan sama matsakaici.
A tsakiyar ƙasa kuma, akwai yiwuwar samun ruwan sama kaɗan a Babban Birnin Tarayya, Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, Neja da Filato.
Haka zalika, a yankin Kudu anyi hasashen yanayi mai zafi da ruwan sama kaɗan a jihohi irin su Oyo, Osun, Ekiti, Ondo, Edo, Enugu, Imo, Abia, Anambra, Delta, Rivers, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom.
NiMet ta gargadi jama’a da su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai yawa, a cire na’urorin lantarki daga soket, a guji zama ƙarƙashin manyan itatuwa, sannan a ɗaure kayayyakin da ba su da ƙarfi.
Haka kuma ta shawarci manoma da su guji amfani da taki da maganin kwari kafin ruwan sama, yayin da ta bukaci kamfanonin jiragen sama da su riƙa samun rahoton yanayi na musamman domin tsara tashi yadda ya k**ata.