02/08/2023
A CIKIN SHEKARU 75 YA YI WANNAN AIKI.
Yana daga cikin baiwar sa, yana da Shekara 21 ya gagari malaman duniya kaf babu sauran Wanda Zai iya karantar da shi, ya yi yawo har ya gaji.
Yana daga cikin baiwar sa, a cikin shekara 75 sai da ya shiga ko ina a duniya, american ne kawai bai samu shiga ba.
Yana daga cikin baiwarsa, a lokaci 'daya, ya musuluntar da mutane dubu goma (10,000) a kasar Ghana, amma turawan kasar England (makirai) sun ce a'a dubu hudu ne (4000) ba goma ba, haka s**a sa a cikin gidan tarihin su (mesuem ) haka American ma s**a sa, amma dai Ko mutum 'daya ya musuluntar an karu dai.
Yana daga cikin baiwarsa, shi-ne mutum na farko da ya ziyarci cibiyar Ilimi ta duniya (azhar) ya kure su, dolen su s**a sallama, kuma ya jagorance su sallar Juma'a, ba a ta6a yin wani bakin fata da ya yi haka ba.
Yana daga cikin baiwar sa, ya ziyarci Sa'ad bin abi wakas(sahabin Manzon Allah S.A.W ) a can cikin garin China, ya kuma ziyarci Imamu Hussain AS a can cikin garin KARBALA (Iraqi ).
Yana daga cikin baiwar sa, shi-ne Wanda ya fara kai addinin masoyin Sa Annabi Muhammadu S.A.W (MUSULINCI ) cikin Kasar RUSSIA, ku binciki tarihi.
Yana daga cikin baiwar sa da albarka, shi-ne ya yi addu'a Allah Ya kora turawan yamma s**a bar AFRICA baki 'daya s**a koma kauyen su, ku binciki tarihi.
Yana daga cikin baiwar sa, Sai da ya musuluntar da PAPA ROMAN zamanin sa na can kasar ITALIAN (shugaba kristoci) hakan ya sa jama'ar sa s**a kashe shi, shi-ma ku binciki tarihi.
Yana daga cikin baiwarsa, Ya wallafa littatafai 75 yana kuma da 'Ya'ya 75 ya rasu yana da shekara 75, Yau Yana da shekara 43 da komawan sa zuwa ga ubangijin sa ma'daukaki, amma Kai kace shi-ne shugaban Kasar duniya, kuma shi-ne ya kawo SUNNAR QABLU Kasashen AFRICA baki 'daya, amma yau a cikin kasa ta NIGERIA 'yan bani na iya gani suke yi sune s**a kawo kabalun.
Kai Abubuwan da yawa ba za su kirgu ba Wallahi, abinda GAUSU BARHAMU ya yi a shekar 75 Wallahi Ko a cikin shekara dubu ne babu Wanda Zai iya kamarsa.