08/11/2025
An gudanar Da Mauludin Manzon Allah (s.a.w.w) Majalisin Tsugugi Da Ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari Zariya...
Daga: Aliiy Usman Nayara
A daren jiya Juma'a 7 ga watan Nuwambar 2025 ne, ƴan uwa Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na majalisin Tsugugi dake ƙaramar Hukumar Sabon Gari Zariya, s**a gudanar da Mauludin Manzon Allah , Annabi Muhammad Rasulullah (s.a.w.w) a kofar gidan Malam Jibril Anakallah, wakilin majalisin ƴan uwa Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Tsugugi
Tunda farko an fara ne da buɗe taro da addu'a, sai aka yi karatun Alqur'ani mai girma, daga bisani aka karanta ziyarar Nabiyul-kareem, sannan aka yi Display, daga bisani kuma Malam Shehu Tsugugi ya gabatar da babban bako mai jawabi wato Sheikh Saluhu Garba.
Yayin jawabin nasa Sheikh Salihu ya yi dogon tsokaci ne akan rayuwa da kyawawan ɗabi'u na fiyayyan halitta (s.a.w.w) a matsayin abin koyi ga dukkan halitta, har wala yau shehin malamin yayi kira ga wajicin haɗin-kai Al'umma Musulmi domin tunkarar kafirci da kafirai duniya.
Bayan kammala jawabinsa ne, Iliyasu Kalifa Shehi Tajul'izzi kano ya gabatar da majalisi , daga bisani kuma Ittihadu-shu'ara s**a gudanar da nasu majalisi ɗin, wanda Malam Ahmad Algwadawy ya jagoranta
Bayan kammala Jawabai da majalisi ne aka yi addu'a aka sallami kowa Alhamdulillah. Anyi an fara taron lafiya an tashi lafiya . Daga kasa wasu daga cikin hotunan yanda taron ya gudana ne.
©Zaria Media Forum
08112025