Waseela

Waseela Domin samun Ingantattun labarai da Rahotanni a harshen Hausa

A garin Zaria kwanaki 3 gudanar da zafafan Muzaharorin Allah wadai da harin ƴan share wuri zauna a IranJiya Talata 14 Ra...
04/03/2026

A garin Zaria kwanaki 3 gudanar da zafafan Muzaharorin Allah wadai da harin ƴan share wuri zauna a Iran

Jiya Talata 14 Ramadan 1447 dai dai da 3 Mar 2026 ƴan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (h) sun ci gaba da Muzahara Allah wadai da ƙasar Amerika da Isra'ila, tare da nuna goyon bayan Jamhuriyar Muslumci a Garin Zariya

Ƴan uwa Musulmi sun Cika kwanaki 3 su na gudanar da muzakarorin, inda a jiyan sun fara Muzahara ne daga ƙofar doka s**a ɗauki hanya cikin shiga garin a dai dai lokacin da s**a isa bakin babban kasuwa zariya s**a tsaya, ƴan uwan na tafiya na kiyaren, Allah wadai da harin haɗin gwaiwar Amerika da Isra'ilan a Jamhuriyar Muslumci Iran,

Harin wanda ya yi sanadiyyar rasa Babban Jagoran Juyin Juyahalin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali khamene'i da manyan ƙwamandojinnkare Muslunci

© Zaria Media Forum
04 - 03 - 2026

Ofishin Sheikh Zakzaky ya fitar da sanarwa Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya raba kayayyakin abinci ga mabuƙata kama...
19/02/2026

Ofishin Sheikh Zakzaky ya fitar da sanarwa Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya raba kayayyakin abinci ga mabuƙata kamar yadda ya saba.

Kamar yadda aka saba duk shekara a lokacin gabatowar watan azumin Ramadana, Jagora (H) na raba kayayyakin abinci ga mabuƙata, a bana ma ya yi rabon abincin a Zariya da wasu garuruwa a fadin kasarnan. Kuma za a ci gaba da wannan rabo har cikin azumin Ramadan na bana.

Rabon kayan abincin ya soma gudana ne tun gabanin shiga watan Ramadana har ya zuwa yau Alhamis 2 ga watan Ramadan, 1447 daidai da 19 ga watan Fabarairun din 2026.

An soma gudanar da shi ne tunda misalin ƙarfe 8 na safiya. Kayayyakin abincin da aka raba sun haɗa da; gero, masara, shinkafa, suga da sauran su.

Aliiy Usman Nayara

YANZU-YANZU: Hotonan Sheikh Sani Khalifa yayin tafiya hutun rabin lokaci, kafin a yanke hukumci, Kotun garin Abuja na ji...
12/02/2026

YANZU-YANZU: Hotonan Sheikh Sani Khalifa yayin tafiya hutun rabin lokaci, kafin a yanke hukumci, Kotun garin Abuja na jiran bayyanar Sojan daya bada umarnin a tsare Sheikh Sani Khalifa bayan zargin da ake masa da sa hannu a Yunkurin Juyin mulki.

Aliiy Usman Nayara

”MU BAMU DA SAƁANI AKAN AL-ƘUR’ANI”Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya ce: “Kuma ba mu da saɓani akan Alƙur’ani. Duk da za ku...
05/02/2026

”MU BAMU DA SAƁANI AKAN AL-ƘUR’ANI”

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Ya ce: “Kuma ba mu da saɓani akan Alƙur’ani. Duk da za ku ji zancen wawayen gari suna cewa akwai wasu masu Alƙur’ani daban, amma fi’ilan dai Alƙur’ani ƙwara ɗaya ne, ba ƙari ba ragi.”

“Amma al’umma ta saɓa akan fassaran Alƙur’ani da kuma ruwayoyi. Don haka aka samu abinda ake ce ma Firƙa An samu FirƘoƙi, an samu Mazhabobi, an samu ƊariƘoƙi. Duk wannan a cikin addinin suke.”

__Bangaren Jawabin Jagoran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda ya gabatar a Iran ta hanyar bidiyo na rufe taron Makon Hadin Kan Musulmi, wanda ya gudana a Abuja, a ranar Laraba 17 ga Rabi’ul Awwal, 1447.

Alƙalamin:Mahadee Musa Aliyu
©ZARIA MEDIA FORUM

Mauludin Imam Mahdi (Aj) da Sayyid Ibraheem Zakzaky (h) a Madarasatul Darul-mahdi Sabon Gari ZariyaDaga Aliiy Usman Naya...
04/02/2026

Mauludin Imam Mahdi (Aj) da Sayyid Ibraheem Zakzaky (h) a Madarasatul Darul-mahdi Sabon Gari Zariya

Daga Aliiy Usman Nayara

Da yammacin yau Laraba 16 sha'aban 1447 dai-dai da 04/02/2026 Makaranta Darul-mahdi (aj) ta gudanar da Mauludin Nisfu Sha'aban a Muhallin Makarantar da Yan awaki, Muciya, Sabon Gari, Zariya

Bayan buɗe taro da Addo'a, aka karanta Alqur'ani mai girma, sai karanta ziyara Imam Mahdi (aj) domin samun tabarrukin kasan cewarsu a wajen taron.

Sheikh Abbas Aljafari, Shine babban baƙo mai jawabi,wanda ya yi jawabin akan Maudu'i mai take 'Alaƙar da'awar Sayyid Zakzaky da Bayyanar Imam Mahadi (aj)' Shehin Malamin ya yi jawabi sosai dangane da alaƙar da'awar Jagora Zakzaky (h) da na Ƙarshe Cikin Limamam Shiriya Imam Mahdi (aj)

A yayin jawabin, ya jawo hankalin Ɗaliban makarata tare da jaddada masu cewa; Duk abinda Sayyid Zakzaky yake tafiya akai shine abinda Imam Mahdi (Aj) zai tafi dashi, idan ya yi Zuhuri domin babu banbanci tsakani, Kamar yadda Sayyid Zakzaky (h) yasha faɗi, daga imam Mahdi (aj) suke samun irshadin Da'awa.

Bayan kammala jawabin Sheikh Abbas Aljafari,sai aka raba walima tare da Addo'a aka tashi.

©ZARIA MEDIA FUROM

RAHOTO: Yadda Mauludin Sayyida Zahra (As) da Imam Ali (As) ya gudana a Sabon Gari Zariya Daga Muhammad Abdullahi HassanD...
29/01/2026

RAHOTO: Yadda Mauludin Sayyida Zahra (As) da Imam Ali (As) ya gudana a Sabon Gari Zariya

Daga Muhammad Abdullahi Hassan

Da yammacin ranar Talata 8 ga watan Sha’aban 1447, 27 Janairu 2026 Iyalan gidan Alhaji Isah mai kifi s**a gudanar da taron Maulidin Sayyida Zahra (As) da Imam Ali (As) a Ƙofar gida Alhaji Isa dake Hayin Ojo Ƙaramar Hukuma Sabon Gari Zariya

Anfara buɗe taro da addu'a aka yi karatun Alqur'ani, Sister Khadija Isa ta karanta ziyarar Sayyida Zahra (as) da Imam Ali (As) a yayin Taron Mauludin.

Malama Hafsah Jushi na gada cikin mayan baki, Masu gabatar da Jawabi a taron, Malama tayi jawabi akan Rayuwa Sayyida Zahra (As), A lokacin da Malama take jawabi ta taɓo Janibobin daban-daban daga cikin Rayuwa Sayyada Zahra (as)

Prof. Ibrahim Taheer chikaji wanda yayi jawabi na biyu, akan Imamuna Ali (As), Sheikh yayi jawabi mai zurfin gaske dangane da imam Ali (as), tare da bayyana jarumar da sadaukarwa, da girma matsayin da Allah (s) ya bashi tun a nan Duniya

Malami daya gabatar da jawabi bayan kammala jawabin Prof Ibrahim, shi ne Malam Sunusi Mai Ashafa, ya gabatar da jawabin akan Maudu'i ma taken 'Muhimmanci Haɗin-kan Al'ummar Musulumi' Ya yi jawabi sosai, inda yace "haɗin-kan Musulumi, Allah (s) ya umarce mu da mu haɗa-kai waje guda, wanda ya kauce ya sani ya sabawa Allah.

Ya ƙara da cewa; Al'umman Musulmi da muna bin umarnin Allah da bazamu rarraba ba a tsakaninmu. Haɗin-kai shine hanya ɗaya ta samun tsira gobe kiyama gaban Allah.

Bayan kammala gwala-gwalan jawaban da Malama s**a yi, Hujjatul-Islam Malam Abdullahi Annahwy ya rufe taro da addu'a.

Bayan dawowa daga Sallah an gudanar da majalisai wanda Iliyasu Khalifan Shehi Mai Tajul'izzi, da Shamsudden Fudiyyah s**a gabatar da Majalisi zuwa illamasha'Allah

© ZARIA MEDIA FORUM

Ba ka taba jin muryar Sheikh Ibraheem Yaƙoub Alzakzaky Hafizahullah ba na Minti 30, amma ba ka da abin zagi sai shi. An ...
26/01/2026

Ba ka taba jin muryar Sheikh Ibraheem Yaƙoub Alzakzaky Hafizahullah ba na Minti 30, amma ba ka da abin zagi sai shi.

An ya kana zaton idan za a muku hisabi a kan zagin da kake masa za ka kai labari kuwa a ranar gobe ƙiyama.?

Idan za ka yi wa kan ka adalci idan ka ji ana faɗar magana a kan mutum, kusantar shi ake yi a tabbatar da abin da aka faɗa a kan shi gaskiya ne.

Duk wanda yake yarda da abin da wani ya kawo mishi kai tsaye na s**ar wani ba tare da bincike ba, sunan shi mai baccin ƙwaƙwalwa.

Me yasa suke baƙanta shi a fuskar ku, kuma suna hana ku sauraren shi da kusantar shi.?

Me hankali ya yi wa kan shi tambaya.?

-Aba Sajjadi.

HOTONA: Yadda wata Amaryar ta gabatar da taron mai kamar Yaumul Qur'an wanda Ƴan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibraheem Z...
26/01/2026

HOTONA: Yadda wata Amaryar ta gabatar da taron mai kamar Yaumul Qur'an wanda Ƴan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (h) suke yi kafin daura Aure a bikinta.

Wanne Fata zakuyi mata

Aliiy Usman Nayara

HOTO
26/01/2026

HOTO

Sayyid Hamid, Ga dukkan alamu baka taba ganin hoton nan ba. A yayin Jana'izar Yayar mahaifiyar Sayyid Zakzaky (h) Hajiya...
25/01/2026

Sayyid Hamid, Ga dukkan alamu baka taba ganin hoton nan ba. A yayin Jana'izar Yayar mahaifiyar Sayyid Zakzaky (h) Hajiya Fadima Aliyu, 28-june-2012.

Sheikh Ibraheem Zakzaky h. 🇳🇬🇵🇸
25/01/2026

Sheikh Ibraheem Zakzaky h. 🇳🇬🇵🇸

Matasa Ƴan Gwagwarmaya tabbatar Addinin Muslumci Ƙarƙashin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (h) Aliiy Usman Nayara
24/01/2026

Matasa Ƴan Gwagwarmaya tabbatar Addinin Muslumci Ƙarƙashin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (h)

Aliiy Usman Nayara

Address

Sabon Gari

Telephone

+2348068113532

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Waseela posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share