29/01/2026
Da ɗumi-ɗumi:
Gwamna Abba na shirin maye gurbin Mataimakin sa da Murtala garo a wani yunkuri na saye zuciyar Ganduje.
Rikici na siyasa ya fara daukar sabon salo a Jihar Kano bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, inda rahotanni ke nuna cewa shiri ya yi nisa na maye gurbin Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamrad Abdulsalam Gwarzo.
Majiyoyi masu tushe a bangaren gwamnatin jihar Kano sun bayyana cewa ana shirin maye gurbin Gwarzo da Alhaji Murtala Sule Garo tsohon ɗantakarar Mataimakin Gwamna zaben 2023, a wani yunkuri da ke nuni da tafiya da cikakken tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
A cewar majiyar, tun farko an tsara wannan sauyi ne la’akari da karfin mabiya da Murtala Garo ke da shi a jam’iyyar APC, tare da kusancinsa da Ganduje, lamarin da ake ganin zai ba tsohon gwamnan damar taka muhimmiyar rawa wajen karfafa gwamnan Abba Kabir Yusuf, musamman ta fuskar siyasa da batun tazarce ba tare da rikici ba.
Wata majiyar ta kara da cewa, akwai wata yarjejeniya ta sirri da ke nuni da cewa bayan kammala wa’adin mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaben shekarar 2031, zai goyi bayan Murtala Sule Garo domin gaje kujerar gwamna, bisa fahimtar da aka cimma tsakanin bangaren gwamnan da gidan Ganduje.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Kano ta fara bayyana matsayinta a fili, inda ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai ta nuna cewa ba za ta iya ci gaba da tafiya tare da Mataimakin Gwamnan KwamradAbdulsalamGwarzo, tare da bukatar ya yi murabus domin gwamnati na buƙatar sirri tare da bawa sabuwar tafiyar siyasa damar samun karbuwa cikin sauki.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin siyasar Kano na shiga sabon zagaye, wanda ka iya sauya taswirar karfin jam’iyyun siyasa da manyan ‘yan wasa kafin manyan zabuka masu zuwa.