07/02/2025
Rana ita yau 15 ga Sha'aban, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) zai cika shekaru 74 da haihuwa. A yayin da aka shafe kusan shekaru 48 yanzu haka yana wannan Da'awar ta kira zuwa ga komawa tafarkin Allah Ta'ala da bin tsarinSa. Wanda yake nufin tun yana matashi dan shekaru 26 yake wannan Da'awar.
Dattijon nan bai huta ba, mutum ba zai san haƙiƙanin Mazlumiyar Jagora (H) ba, har sai ya ji sashinsu daga gare shi. A takaice, ko a jawabin da ya yi na karshen nan ga Harisawa, ya yi bitan wasu daga waki'o'i da kame-kamen da azzaluman mahukuntan kasar nan s**a masa, wanda samun cikakken bayanai akansu zai zo a littafan da ya rubuta da kansa don ba da tarihin rayuwa da gwagwarmayarsa.
Idan mutum yana iƙirarin shi almajirin wannan Dattijon Bawan Allah din ne, to duk almajiri zai so tausayawa Malaminsa wajen ganin ya rayu cikin natsuwar zuciya, da lafiyar jiki, da yalwataccen dama na fuskantar matsalolin da ke fuskantarsa.
Kamar zai zama akwai rashin kunya na ƙarshe, mutum ko da ya kai sa'an Jagora (H) a shekaru, ko ya girme shi, in dai yana raya cewa shi mabiyansa ne, Jagoran ya yi wata matsaya, shi ya tsaya yana guna-guni da ƙoƙarin nuna in kaza ne, to ai kaza, ko tuhumar me zai sa kaza, mu ai kaza. Ballantana wannan ɗin ya zama yaro ne da bai kai ko shekaru 40 ko ma 30 ba. Ina ma mutum rantsuwa da Allah, ko a zuciyarsa ya ji wani ɗar, ko zafi, ko kokonto, to ya samu matsala, ya dage da Istigfari da addu'ar tabbatan Imani a zuciyar.
Sauƙaƙaƙƙen bayani Jagora (H) ya yi a cikin abin da bai wuce awa 1 ba, ya fitar da komai dalla-dalla, har ma da dalilai. Kuma ya ba da uzuri, akan cewa sun yi hakan ne da nufin gyara, ba su yi don su batawa kowa rai ba. Wannan fa k**ar rarrashi Jagora yake yi, wanda a wajenmu, abin jin nauyi ne ma hakan. Kuma Jagoran nan, wadanda s**a je gabansa sun ga dukkan karamci da mutuntawa da ya musu, an yi nishadi da farin ciki, an gaisa cikin sakin fuska, an sha shayi, an ci abinci, har ma sai da ya bi kowa a duk mutanen da s**a je da Hadiyya ta musamman.
Ba za mu taimaki kanmu ba mu kasance cikin amincin Allah Ta'ala da karban matsayar wanda muke cewa shi ne silan shiriyarmu a duniya da dacewarmu a lahira? Wai me ma aka yi ne na ɓaci? Bisa sa'ayin wasu 'yan uwa, a bayan Waki'a, Jagora na tsare, sun rika ƙirƙiran rundunoni daban-daban, wasu da Iklasi s**a ƙirƙira, Allah Ya sani, wasu kuma da manufa. Kuma har bayan fitowar Jagora ba an daina ƙirƙiran ba ne, duka kuma da sunan Harka Islamiyya ƙarƙashin Jagorancinsa (H), mene ne aibu idan yace duka a dakatar da su, babu bukatarsu, in da bukatar nan gaba zai samar da kansa ko bisa Irshadinsa?
Wasu suna guna-guni akan Jaishi Shaheed Ahmad (JASAZ) wadda take ƙarƙashin Mu'assasatu Abul Fadl Abbas, cewa ita ma bayan Waki'a aka samar da ita. Eh haka ne, bayan Waki'a ne, amma tun samarwar, har ta kafu, har zuwa cigabanta duk da masaniya da irshadin su Jagora (H) ake yinta. Ba wasu ne kawai s**a ƙirƙira don kansu suke gudanarwa don kansu ba ba tare da kai bayanansu inda ya dace ba. Saboda haka, in an samar da wata runduna, komai kyawun sunan da aka saka mata, in ya zama bata da tushe ko sila da Jagora, me zai sa ka yi tsammanin dole ya amshe ta?
Harka na da tsari da nizami, a hankalce in kowa zai zama yana da damar ya ƙirƙiri runduna ko tawaga an san shi ko ba a san shi ba, su rika saka kaya suna Display ko Fareti, ko su zo wajen taron Harka suna raba Duty, za a wayi gari Maƙiya ko Jahiliyya za ta samar da nata, sai a fara ɓarna da rigima, irin wanda ba tun yanzu ba ya fara aukuwa. Ƙarshe su je suna wani abin mare kyau wanda Harkar za a kalla da shi. Saboda haka, in har mutum na da tunani, ko da yana wata Jaishu ko Runduna, ko Mu'assasa ire-iren wadannan da basu da 'stamp' din Jagora (H), sai Jagora ya ankarar da shi hatsarin hakan, zai yi godiya ga Allah ne, ya yi fatan Allah Ya karbi sa'ayinsa da ya gabata a wannan rundunar, Ya yafe masa gazawarsa, sai ya watsar da ita.
Akan haka nake jinjina ga masu gudanar da JAISHU ƘAASIM SULAIMAN, bisa bayyana matsayarsu na rushe rundunar, da fatan Allah Ya karbi kokarinsu. Haka ma na ga JAISHU ALIYUL AKBAR su ma sun yi takarda da ke nuna sun dakatar da duk wani activities da suke karkashin wannan sunan. Dazu ma na ga Sanarwar ANSARU ZAKZAKY (H) sun dakatar da ayyukansu a ƙasa bakidaya. Allah Ya girmama lada gabadaya. Ya karbi sa'ayi.
Akwai Jaishohi da Rundunoni, da Ƙungiyoyi sun fi 20 da aka samar, wanda dukkansu akwai bukatar su karbi Irshadin su Jagora (H), ko sun bayyana a Public ko basu bayyana ba, su dakatar da duk abubuwan da suke yi. Mambobinsu su koma su shiga wasu Lajanoni da ake da su a cikin Harka Islamiyya, k**ar Dandalin Matasa in dai mutum bai kai shekaru 40 ba, ko Academic Forum in shi ɗalibi ne ko Malami, ko Sisters Forum in mace ce matashiya ko tsohuwa, ko Resource Forum in ma'aikaci ne, ko Huffaz Forum in mahaddaci ne ko mai niyyar haddan, ko Ittihadu in mawaki ne, ko Ahluddusur, in kai dan kasuwa ne ko manomi ko mai kudi, ko ISMA in mai karanta bangaren kiwon lafiya ne, ko ma in duk ba zai yi su ba ya zama cikin Brothers Forum ya yi ta ba da gudummawa a Da'irarsu.
Jagora (H) ya taba bamu misali da shirya taro, inda yace tana iya yiwuwa mai dafa shayi ko abincin da za a ci a wajen taro, ya fi Malamin da ya yi jawabi a wajen taron lada a wajen Allah Ta'ala, in ya fi shi yi da Iklasi. Haka ma mai shirya takalma ko ababen hawa, ko mai gyara shimfida. Aiki a Harka akwai bigiren yinsa da dama fa. Ga Fudiyya nan tana bukatar masu ba da gudummawar koyarwa.
Idan kuma mutum ma yana sha'awar kasancewa a wani waje ne da ake Fareti ko Display, zai iya kwankwasa JASAZ, idan sun tashi diban ma'aikata, in ya cika sharuddansu sai su dauke shi. Ko kuma ya jira Harisanci ta bude ƙofar diban sababbin Harisawa, sai ya shiga shima in zai iya cike sharudda.
Babu bukatar hargowa da hayaniya sam. Ko da muke ganin muna garuruwanmu ne, amma in muka zo muna hayaniya a Social Media akan wani abu da mun tabbatar matsayar Jagora ne, kuma mun tabbatar Jagora din nan yana tare da ku har a Media din, to k**ar muna gabansa ne muna masa hayaniya da hargowa irin yadda wasu s**a ma Annabi (S) a yayin jinyarsa na ajali. Sai mu kasance cikin tsinuwar Allah Ta'ala. Allah Ya tsare mu.
Mu yi haƙuri, mu yi sa'ayi, mu dinke kanmu, mu daina ganin akwai bangare biyu a Harka, kuma muna ɓangare kaza ne, kowa ya ji Harka abu guda ce, kuma Jagoranta shi ne Sayyid Zakzaky (H), mu so shi, mu ƙaunace shi, mu taimake shi akan Da'awar da yake yi, har mu riski ajali ta hanyar karbabbiyar Shahada insha Allah, ko ta hanyar cikawa da imani.
Wadanda aka ba Mas'uliyyar, duk girmanta da bayyanarta, fata shi ne a yi aiki saboda Allah, k**ar yadda na kawo a sama, mai dafa shayi a Markaz ya ba mutane su sha, ko mai jera takalman masu zuwa Ta'alimi, ko mai hada na'ura, duk suna iya fin Kwamandan Harisawa, ko su fi Amir matsayi da daraja da fifikon lada a wajen Allah Ta'ala. Saboda haka Mas'uliyyar Harka Islamiyya amana ce kawai, Nauyi ne, ba matsayi ba ne. Zai zama matsayi ne ga mutum kawai a Lahira in ya kyautata yinsa. Allah Ya dafa mana.
— Saifullahi M. Kabir
8 Sha'aban 1446
7 February 2025