08/10/2024
JAGORA (H)💓
Idan muka ce Jagora, muna nufin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).
A wajen mu shine sanadin shiryar mu, ba don muna ganin wadanda ba mu ba a matsayin batattu, sai don daga abin da muka fahimta bayan amsa Da'awarsa shine, ba don shi ba, da ba mu riski alkairai masu yawa na duniya da lahira ba.
Sanadin sa muka san Allah da yadda za mu bauta masa, muka san Manzon Allah (S) da irin yadda ake sallama masa, muka san A'immatu Ahlulbaiti (AS) da wajabcin riko da su a bayan Annabi (S).
Jagora na nufin Jagoran Gwagwarmayar yunkurin kawar da tsarin Kafirci wacce Bature ya dankara mana, da dawo da ikon addinin Musulunci a doron kasa ta yadda adalci da walwala zai shimfiɗu a doron ƙasa.
Malami ne da dukkan ma'anar Malunta. Idan ka dauka Haddar Alkur’ani ne Malunta, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mahaddacin Alkur’ani ne. Idan sanin Luggar Larabci ko sanin Fiqihu ko Aqida ko Tafsiri duk Shaikh Zakzaky Malami ne a bangarorin. Idan bangaren ilimin da ake cewa Boko ko na zamani ne, nan ma masani ne a bangaren.
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi karatun littafan addini daban-daban a wajen malamai daban-daban na Shi'a da Sunnah sama da 20 a ƙasar nan da wajenta, tun shekarun yarinta har zuwa tsufa. Wanda Insha Allah zan kawo suna yansu wani lokaci.
Shaikh Zakzaky (H) masoyin Manzon Allah (S) ne, don haka ma a rayuwarsa tabbataccen abu ne ya je Makkah da Madina ya ziyarci Makwancin Manzon Allah (S) sau 20. Cikinsu Shaikh Zakzaky ya je aikin Hajji sau 8, ya yi Umra sau 4 (a wasu watanni), sannan ya yi kwanaki 30 din Ramadan din shekaru 8 a tsakanin Haramin Allah Ta'ala da na Annabi (S).
Ya ziyarci duk A'immatu Ahlulbaiti (AS) a makwantansu a Madina, Iraq da Iran, ba sau daya ko biyu ba, yana mai sanin hakkinsu, da sallamawa Shugaban cin su.
Shaikh Zakzaky daga abin da muka iya tabbatarwa shine kusan fiye da rabin Rana kun shekarar sa yana azumtarsu ne. Domin tun yana matashi har tsufansa, har yanzu haka ya kan azumci watanni Rajab, Sha'aban da Ramadan a jere, sannan yana azumtar Litinin.
Ahmad Assaminaky