17/05/2025
YANZU YANZU: Yan Bindiga Sun kusa k@she Ni a jihar Kaduna Allah ya tseratar dani, inji Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma wanda ya kafa Jami’ar American University of Nigeria (AUN), Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya tsira daga yunkurin kashe shi a Jihar Kaduna.
Atiku ya ce ya ɓoye matarsa da ’ya’yansa a cikin kabad (wardrobe), inda ya fuskanci waɗanda s**a zo su kashe shi. Ya bayyana cewa sun harbe shi amma harsashensu bai same shi ba.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga daliban da ke kammala karatu a AUN a ajin 2025.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya kuma tuna yadda gwamnatin soja a wani lokaci ta ba shi kujerar gwamna ba tare da an yi zaɓe ba.
Ya ce ya ƙi karɓar tayin, amma daga baya ya samu kujerar mataimakin shugaban ƙasa a shekarar 1999 ta hanyar da ta dace.
A cewarsa:
> “Na ɓoye matata da ’ya’yana a cikin kabad, sai na fito na fuskanci waɗanda s**a shigo. Sun harbe ni amma s**a ci kuskure. Na tashi na ce, ‘Me ya sa kuka harba?’ Wannan shi ne jarumta.
> “Na fuskanci ƙalubale da dama. An far wa rayuwata, amma ban taɓa ja da baya ba.
> “Haƙuri ba rauni ba ne. Makamin masu hikima ne. A lokacin da muke adawa da mulkin soja, sun ba ni kujerar gwamna ba tare da zaɓe ba, na ƙi karɓa. Amma a 1999, na samu ta halastacciyar hanya kuma na zama Mataimakin Shugaban Ƙasa.”
Ya kuma tuna yadda ya koyi jarumta daga ubangidansa, marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua, wanda ya fuskanci hukuncin kisa ba tare da tsoro ba.
> “Ranar da aka shirya kashe shi, jinin sa yana daidai. Wannan soja ne. Wannan shi ne jarumta,” in ji Atiku.