
06/09/2025
Ƙungiyar Matasan Arewa ta nemi a ɗauki mataki akan Sanata Shehu Buba kan zargin sa da hannu a ta'addanci
Ƙungiyar Ci-gaban Matasan Arewa AYM, ta kirayi Sufeto-Janar na ƴan sanda (IGP) da ya gaggauta ɗaukar matakin doka akan Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Umar Buba, bisa zargin sa da tallafa wa ayyukan ta'addanci a garuruwan Arewacin Nijeriya.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Kakakinta, Kwamared Yahaya Muhammed Garba, AYM ta bayyana kaɗuwarta game da ƙamarin ayyukan ta'addanci da ke ƙoƙarin mamaye shiyyar ganin yadda ake rasa rayukan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba a kullum.
Ta ce, ƙalubalen da al'umma ke fuskanta a sanadiyyar ayyukan ƴan bindiga da ɓarayin daji na garkuwa da ta'addanci akan dukiyoyinsu ya zama ruwan dare a sassan jihohin ƙasar, lamarin da ya ɗaiɗaita mutane da dama daga muhallansu da jefa su cikin tsoro.
A cewarta, hakan ya yi mummunan tasiri ga haɗin kan al'umma da tattalin arziƙi, wanda ya jefa iyalai da dama cikin matsi akan matsin da suke fuskanta sakamakon taɓarɓarewar harkokin tattali a ƙasar.
Ta ƙara da cewa, ayyukan garkuwa da mutane da neman a biya kuɗaɗen fansa ya zama babban kasuwanci ga masu aikata manyan laifuka, saboda amfani da hakan wajen harin mutane da ɓangarorin daban-daban wanda ya zama sababin ɗaiɗaita dubunnan mutane da iyalansu.
Har'ilayau AYM ta yi tsokaci da jinjina akan matakan da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka wajen ganin tsaro mai ɗorewa ya samu a shiyyar da s**a haɗa da ƙara jami'an sojoji da ƴan sanda da sauransu a wuraren da ke fama da rashin tsaro.
Saidai, AYM ta bayyana ayyukan ire-iren Sanata Shehu Buba a matsayin abinda ka iya daƙile ƙoƙarin gwamnati na kawo ƙarshen matsalar.
A kwanan nan aka ga wani faifan bidiyo yana nuna kuɗaɗe da babura da aka tura daga gidan Sanatan zuwa wajen ƴan bindiga a Zamfara, lamarin da ke ƙoƙarin tabbatar da zargi akansa da hannu a ayyukan ta'addanci a shiyyar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.