02/02/2024
*KU KOYAWA YARANKU HALAYE UKU*:
1. Yawan gaishe da na gaba dasu.
2. Nutsuwa da barin wasa ahanya.
3. Futa cikin kyakykyawar shiga.
*KU HANA YARANKU HALAYEN NAN*:
1. Yawan yawace-yawace.
2. Yawan Abokai/kawaye barkatai.
3. Rashin kunya da fadace-faface.
*KU RIKA GWABE BAKIN YARANKU*:
1. Idan suna sa baki a maganar manya
2. Idan suna kawo tsegumi da gulma.
3. Idan suna zagi ko karyata manya.
*KUYI MUSU HORO ME TSANANI*:
1. Idan suna wasa da Sallah.
2. Idan s**a fara kwadayi da roko
3. Idan s**a fara karya da lalaci.
*KU KARA JAWO YARANKU JIKI*:
1. Idan s**a balaga.
2. Idan basu da lafiya.
3. Idan kuna gida a zaune.
*KU KWADAITAR DA YARANKU*:
1. Nacin karatu da rubutu.
2. Dagewa wajen cimma buri.
3. Lada da nasara in anbi hanyar Allah.
*KU NUNAWA YARA MUHIMMANCIN*:
1. Riko da Addinin musulunchi.
2. Zumunchi da ziyarar dangi.
3. Lafiya, Lokachi da chance/kuruciya.
*KU DAINA WADANNAN AGABANSU*:
1. Bayyana tsiraici/mu'amalar aure
2. Wasan banza na kuruciya, kallo.
3. Bayyana rashin jituwa atsakaninku.
*KU YAWAITA AGABAN YARANKU*:
1. Karatun Alqur'ani da salloli.
2. Aikata gaskiya da Rukon Amana.
3. Wadatar zuci da godiyar Allah.
*SUKE JIN TSORON KU TA HANYAR*:
1. Tsawatar musu in sunzo da wargi.
2. Rashin barinsu babu abinyi.
3. Taqaita nuna musu so kuru-kuru.
*KU DAGE KU CIREWA YARANKU*:
1. Tsoron mutuwa.
2. Tsoron talauchi.
3. Tsoron wanda baya tsoron Allah.
*KU GOYI BAYAN YARANKU INHAR*:
1. sune ke da gaskiya.
2. Ba sa6o s**a aikata ba.
3. sunyi abu domin kare mutuncinku.
*KUKE TSORATAR DA YARANKU*:
1. Illar Hadama.
2. Futinar rigima.
3. Hadarin taqama da girman kai.
*KU RIKA SANARDA YARANKU*:
1. Asali da Tarihi.
2. Mutuwa da kabari.
3. Dadi da rashin sa.
*KU BAWA YARANKU HORO NA*:
1. Taqaita cin abinchi.
2. Karancin Barchi da zaman hira.
3. Watsarda dogon buri da sharholiya.
Allah yasakawa iyayenmu da alkhairee.