13/08/2025
Tinubu Zai Ci Gaba da Ƙarfafawa NDLEA Wajen Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi – Ribadu
Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ci gaba da ƙarfafawa Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) saboda muhimmancin ta wajen nasarar tsare-tsaren tsaron ƙasa. Ya bayyana haka ne a lokacin ƙaddamar da sabbin motocin aiki 48 ga manyan ofisoshin sassa na NDLEA a fadin ƙasar, a Abuja ranar Laraba. Ribadu ya yaba wa shugaban hukumar, Manjo Janar Buba Marwa (Rtd), bisa jajircewa da tsayuwa tsayin daka wajen yaƙar matsalar miyagun ƙwayoyi da ke barazana ga tsaro, zaman lafiya da lafiyar jama’a.
Ribadu ya ce ƙaruwar kayan aiki da tallafin da Shugaba Tinubu ke bayarwa ya taimaka wajen inganta ayyukan hukumar, ya kuma bayyana cewa fataucin miyagun ƙwayoyi na da alaƙa kai tsaye da matsalar tsaro a ƙasar nan, inda ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu daga haramtattun ƙwayoyi. Ya ƙara da cewa motocin za su taimaka wa NDLEA wajen ƙarfafa sa ido, da tabbatar da cewa ba wanda ya tsere cikin masu aikata laifi daga hukunci.
A nasa jawabin, Marwa ya bayyana cewa wannan lamari alama ce ta ci gaba wajen maida NDLEA hukuma ta zamani mai inganci da ƙima a idon duniya. Ya gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar, yana mai cewa ƙaruwar motocin aikin na nuna jajircewar gwamnati wajen magance tushen matsalar rashin tsaro da tabarbarewar zamantakewa. Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin shirin Renewed Hope, Shugaba Tinubu ya sanya tsaron ƙasa, gyaran hukumomi da kare rayukan ‘yan ƙasa a matsayin ginshiƙai na gwamnatinsa.